This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah Al-Qari'ah (The Striking Hour).
ٱلۡقَارِعَةُ
﴿١﴾
Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!(1)
Tafseer:
مَا ٱلۡقَارِعَةُ
﴿٢﴾
Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?(2)
Tafseer:
وَمَاۤ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡقَارِعَةُ
﴿٣﴾
Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?(3)
Tafseer:
یَوۡمَ یَكُونُ ٱلنَّاسُ كَٱلۡفَرَاشِ ٱلۡمَبۡثُوثِ
﴿٤﴾
Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.(4)
Tafseer:
وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ ٱلۡمَنفُوشِ
﴿٥﴾
Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.(5)
Tafseer:
فَأَمَّا مَن ثَقُلَتۡ مَوَ ٰزِینُهُۥ
﴿٦﴾
To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.(6)
Tafseer:
فَهُوَ فِی عِیشَةࣲ رَّاضِیَةࣲ
﴿٧﴾
To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.(7)
Tafseer:
وَأَمَّا مَنۡ خَفَّتۡ مَوَ ٰزِینُهُۥ
﴿٨﴾
Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).(8)
Tafseer:
فَأُمُّهُۥ هَاوِیَةࣱ
﴿٩﴾
To, uwarsa Hãwiya ce.(9)
Tafseer:
وَمَاۤ أَدۡرَىٰكَ مَا هِیَهۡ
﴿١٠﴾
Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?(10)
Tafseer:
نَارٌ حَامِیَةُۢ
﴿١١﴾
Wata wuta ce mai kuna.(11)
Tafseer: