Surah Al-Asr (The Time)

Surah Al-Asr (The Time)

Hausa Translation3 Aya count
This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah Al-Asr (The Time).
وَٱلۡعَصۡرِ ﴿١﴾
Ina rantsuwa da zãmani.*
* Wasu suna fassarawa da lokacin sallar La'asar da kuma marece. A kõwane dai, an bai wa lokaci muhimmanci, zãmani yana yanke wanda bai yanke shi ba. ba ya halatta ga mutum wata mudda ta zãmani ta wuce shi bai san amfãnin da ya sãma wa kansa a cikinta ba, kuma kõme ya sãmu idan ba addini ba ne, to, hasãrace.
(1)
Tafseer:
إِنَّ ٱلۡإِنسَـٰنَ لَفِی خُسۡرٍ ﴿٢﴾
Lalle ne mutum yana a cikin hasara.(2)
Tafseer:
إِلَّا ٱلَّذِینَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلۡحَقِّ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلصَّبۡرِ ﴿٣﴾
Fãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri (su kam, basu cikin hasara).(3)
Tafseer:

تسجيل الدخول / إنشاء حساب

أدخل بريدك الإلكتروني ليصلك رمز الدخول السريع (بدون كلمة مرور)