قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلۡفَلَقِ ﴿١﴾
"Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya"
مِن شَرِّ مَا خَلَقَ ﴿٢﴾
"Daga sharrin abin da Ya halitta."
وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ ﴿٣﴾
"Da sharrin dare, idan ya yi duhu."
وَمِن شَرِّ ٱلنَّفَّـٰثَـٰتِ فِی ٱلۡعُقَدِ ﴿٤﴾
"Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin kuduri"
وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ ﴿٥﴾
"Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada."