Surah An-Nas (Mankind)

Surah An-Nas (Mankind)

Hausa Translation6 Aya count
This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah An-Nas (Mankind).
قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ ﴿١﴾
"Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."(1)
Tafseer:
مَلِكِ ٱلنَّاسِ ﴿٢﴾
"Mamallakin mutane."(2)
Tafseer:
إِلَـٰهِ ٱلنَّاسِ ﴿٣﴾
"Abin bautãwar mutãne."(3)
Tafseer:
مِن شَرِّ ٱلۡوَسۡوَاسِ ٱلۡخَنَّاسِ ﴿٤﴾
"Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa."*
* Shaiɗan yakan ɓõye idan ya ji an ambaci sunan Allah, dõmin haka aka yi masa suna mai ɓõyewa, wãto bã ya zuwa wurin da ake karatu da wa'azi, kamar yadda bã ya zama cikin zũciyar mutum mai ibãda da gaskiya. Ibãda ta gaskiya ita ce wadda aka yi ta kamar yadda Allah Ya ce a yi ta. Banda ibãdar bidi'a, ba ta korar Shaiɗan. Kuma da sharaɗin a yi ibãdar da kyakkyawar niyya, dõmin aikin da bãbu niyya mai kyãwu game da shi ɓãtacce ne.
(4)
Tafseer:
ٱلَّذِی یُوَسۡوِسُ فِی صُدُورِ ٱلنَّاسِ ﴿٥﴾
"Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane."(5)
Tafseer:
مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ ﴿٦﴾
"Daga aljannu da mutane."(6)
Tafseer:

تسجيل الدخول / إنشاء حساب

أدخل بريدك الإلكتروني ليصلك رمز الدخول السريع (بدون كلمة مرور)