غُلِبَتِ ٱلرُّومُ ﴿٢﴾
An rinjãyi Rũmawa.*
فِیۤ أَدۡنَى ٱلۡأَرۡضِ وَهُم مِّنۢ بَعۡدِ غَلَبِهِمۡ سَیَغۡلِبُونَ ﴿٣﴾
A cikin mafi kusantar ƙasarsu, kuma sũ, a bãyan rinjãyarsu, zã sn rinjãya.
فِی بِضۡعِ سِنِینَۗ لِلَّهِ ٱلۡأَمۡرُ مِن قَبۡلُ وَمِنۢ بَعۡدُۚ وَیَوۡمَىِٕذࣲ یَفۡرَحُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ﴿٤﴾
A cikin'yan shẽkaru. Al'amari na Allah ne a gabãnin kõme da bãyansa, kuma a rãnar nan mũminai zã su yi farin ciki.
بِنَصۡرِ ٱللَّهِۚ یَنصُرُ مَن یَشَاۤءُۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِیزُ ٱلرَّحِیمُ ﴿٥﴾
Da taimakon Allah Yanã taimakon wanda Yake so. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
وَعۡدَ ٱللَّهِۖ لَا یُخۡلِفُ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥ وَلَـٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا یَعۡلَمُونَ ﴿٦﴾
Wa'adin Allah, Allah bã ya sãɓãwa ga wa'adinsa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
یَعۡلَمُونَ ظَـٰهِرࣰا مِّنَ ٱلۡحَیَوٰةِ ٱلدُّنۡیَا وَهُمۡ عَنِ ٱلۡـَٔاخِرَةِ هُمۡ غَـٰفِلُونَ ﴿٧﴾
Sunã sanin bayyanannar rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sũ shagalallu ne daga rãyuwar Lãhira.*
أَوَلَمۡ یَتَفَكَّرُواْ فِیۤ أَنفُسِهِمۗ مَّا خَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَیۡنَهُمَاۤ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَأَجَلࣲ مُّسَمࣰّىۗ وَإِنَّ كَثِیرࣰا مِّنَ ٱلنَّاسِ بِلِقَاۤىِٕ رَبِّهِمۡ لَكَـٰفِرُونَ ﴿٨﴾
Shin, ba su yi tunãni ba a cikin zukãtansu cẽwa Allah bai halitta sammai da ƙasa ba da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya* da ajali ambatacce? Kuma lalle mãsu yawa daga mutãne kãfirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu?
أَوَلَمۡ یَسِیرُواْ فِی ٱلۡأَرۡضِ فَیَنظُرُواْ كَیۡفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِینَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُوۤاْ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةࣰ وَأَثَارُواْ ٱلۡأَرۡضَ وَعَمَرُوهَاۤ أَكۡثَرَ مِمَّا عَمَرُوهَا وَجَاۤءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَیِّنَـٰتِۖ فَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِیَظۡلِمَهُمۡ وَلَـٰكِن كَانُوۤاْ أَنفُسَهُمۡ یَظۡلِمُونَ ﴿٩﴾
Shin, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã dõmin su gani yadda aƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafiya ƙarfi daga gare su kuma suka nõmi ƙasa suka rãya ta fiye da yadda suka raya ta, kuma manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu. Sabo da haka Allah ba Ya yiwuwa Ya zãlunce su, amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
ثُمَّ كَانَ عَـٰقِبَةَ ٱلَّذِینَ أَسَـٰۤـُٔواْ ٱلسُّوۤأَىٰۤ أَن كَذَّبُواْ بِـَٔایَـٰتِ ٱللَّهِ وَكَانُواْ بِهَا یَسۡتَهۡزِءُونَ ﴿١٠﴾
Sa'an nan ãƙibar waɗannan da suka aikata mũgun aiki ta kasance mafi muni, wãtau sun ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma suka kasance sunã izgili da su.
ٱللَّهُ یَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ یُعِیدُهُۥ ثُمَّ إِلَیۡهِ تُرۡجَعُونَ ﴿١١﴾
Allah ne ke fãra yin halitta, sa'an nan Ya sãke ta sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku.
وَیَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ یُبۡلِسُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ ﴿١٢﴾
Kuma a rãnar da sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi zã su kãsa magana.
وَلَمۡ یَكُن لَّهُم مِّن شُرَكَاۤىِٕهِمۡ شُفَعَـٰۤؤُاْ وَكَانُواْ بِشُرَكَاۤىِٕهِمۡ كَـٰفِرِینَ ﴿١٣﴾
Kuma bã su da mãsu cẽto daga abũbuwan shirkinsu, kuma snn kasance mãsu kãfircẽwa daga abũbuwan shirkinsu.
وَیَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ یَوۡمَىِٕذࣲ یَتَفَرَّقُونَ ﴿١٤﴾
kuma a rãnar tashin Alkiyama ranar ne suke rarrabuwa.
فَأَمَّا ٱلَّذِینَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ فَهُمۡ فِی رَوۡضَةࣲ یُحۡبَرُونَ ﴿١٥﴾
To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai to sũ anã faranta musu rãyuka, a cikin wani lambu.
وَأَمَّا ٱلَّذِینَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔایَـٰتِنَا وَلِقَاۤىِٕ ٱلۡـَٔاخِرَةِ فَأُوْلَـٰۤىِٕكَ فِی ٱلۡعَذَابِ مُحۡضَرُونَ ﴿١٦﴾
Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu da kuma haɗuwa da Rãnar Lãhira, to, waɗancan anã halartar da su a cikin azãba.
فَسُبۡحَـٰنَ ٱللَّهِ حِینَ تُمۡسُونَ وَحِینَ تُصۡبِحُونَ ﴿١٧﴾
Sabõda haka tsarkakẽwa ta tabbata ga Allah a lõkacin da kuke shiga maraice, da lõkacin da kuke shiga sãfiya.*
وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَعَشِیࣰّا وَحِینَ تُظۡهِرُونَ ﴿١٨﴾
Kuma Shĩ ne da gõdiya, a cikin sammai da ƙasã kuma da lõkacin yamma da lõkacin zawãli.
یُخۡرِجُ ٱلۡحَیَّ مِنَ ٱلۡمَیِّتِ وَیُخۡرِجُ ٱلۡمَیِّتَ مِنَ ٱلۡحَیِّ وَیُحۡیِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ وَكَذَ ٰلِكَ تُخۡرَجُونَ ﴿١٩﴾
Yanã fitar da mai rai daga matacce kuma Yanã fitar da matacce daga mai rai, kuma Yanã rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta. Kuma haka ake fitar da ku.
وَمِنۡ ءَایَـٰتِهِۦۤ أَنۡ خَلَقَكُم مِّن تُرَابࣲ ثُمَّ إِذَاۤ أَنتُم بَشَرࣱ تَنتَشِرُونَ ﴿٢٠﴾
Kuma akwai daga ãyõyin Sa, Ya halitta ku daga turɓãya, sai gã ku kun zama mutum, kunã wãtsuwa.
وَمِنۡ ءَایَـٰتِهِۦۤ أَنۡ خَلَقَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَ ٰجࣰا لِّتَسۡكُنُوۤاْ إِلَیۡهَا وَجَعَلَ بَیۡنَكُم مَّوَدَّةࣰ وَرَحۡمَةًۚ إِنَّ فِی ذَ ٰلِكَ لَـَٔایَـٰتࣲ لِّقَوۡمࣲ یَتَفَكَّرُونَ ﴿٢١﴾
Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku.* Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni.
وَمِنۡ ءَایَـٰتِهِۦ خَلۡقُ ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَـٰفُ أَلۡسِنَتِكُمۡ وَأَلۡوَ ٰنِكُمۡۚ إِنَّ فِی ذَ ٰلِكَ لَـَٔایَـٰتࣲ لِّلۡعَـٰلِمِینَ ﴿٢٢﴾
Kuma akwai daga ãyõyin Sa halittar sammai da ƙasã da sãɓã, war harsunanku, da launukanku. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mãsu ilmi.
وَمِنۡ ءَایَـٰتِهِۦ مَنَامُكُم بِٱلَّیۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱبۡتِغَاۤؤُكُم مِّن فَضۡلِهِۦۤۚ إِنَّ فِی ذَ ٰلِكَ لَـَٔایَـٰتࣲ لِّقَوۡمࣲ یَسۡمَعُونَ ﴿٢٣﴾
Kuma akwai daga cikin ãyõyin Sa, barcinku a cikin dare da rãna, da nẽmanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu saurãrãwa.
وَمِنۡ ءَایَـٰتِهِۦ یُرِیكُمُ ٱلۡبَرۡقَ خَوۡفࣰا وَطَمَعࣰا وَیُنَزِّلُ مِنَ ٱلسَّمَاۤءِ مَاۤءࣰ فَیُحۡیِۦ بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۤۚ إِنَّ فِی ذَ ٰلِكَ لَـَٔایَـٰتࣲ لِّقَوۡمࣲ یَعۡقِلُونَ ﴿٢٤﴾
Kuma akwai daga cikin ãyõyin Sa, Ya nũna muku walƙiya a kan tsõro da ɗammãni kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu hankaltawa.
وَمِنۡ ءَایَـٰتِهِۦۤ أَن تَقُومَ ٱلسَّمَاۤءُ وَٱلۡأَرۡضُ بِأَمۡرِهِۦۚ ثُمَّ إِذَا دَعَاكُمۡ دَعۡوَةࣰ مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ إِذَاۤ أَنتُمۡ تَخۡرُجُونَ ﴿٢٥﴾
Kuma akwai daga ãyõyinsa, tsayuwar sama da asƙã bisa umurninsa, sa'an nan idan Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasã, sai gã ku kunã fita.
وَلَهُۥ مَن فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ كُلࣱّ لَّهُۥ قَـٰنِتُونَ ﴿٢٦﴾
Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasã Nãsa ne shi kaɗai. Dukansu mãsu tawãli'u ne a gare Shi.
وَهُوَ ٱلَّذِی یَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ یُعِیدُهُۥ وَهُوَ أَهۡوَنُ عَلَیۡهِۚ وَلَهُ ٱلۡمَثَلُ ٱلۡأَعۡلَىٰ فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِیزُ ٱلۡحَكِیمُ ﴿٢٧﴾
Kuma Shĩ ne Wanda Ya fãra halitta, sa'an nan Ya sãke ta kuma sakẽwarta tã fi sauƙi a gare shi. Kuma Yanã da misãli wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasã kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
ضَرَبَ لَكُم مَّثَلࣰا مِّنۡ أَنفُسِكُمۡۖ هَل لَّكُم مِّن مَّا مَلَكَتۡ أَیۡمَـٰنُكُم مِّن شُرَكَاۤءَ فِی مَا رَزَقۡنَـٰكُمۡ فَأَنتُمۡ فِیهِ سَوَاۤءࣱ تَخَافُونَهُمۡ كَخِیفَتِكُمۡ أَنفُسَكُمۡۚ كَذَ ٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡـَٔایَـٰتِ لِقَوۡمࣲ یَعۡقِلُونَ ﴿٢٨﴾
Ya bũga muku wani misãli daga kanku. Kõ kunã da abõkan tarẽwa, daga cikin bãyin da hannãyenku na dãma suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a ciki kunã tsõron su kamar tSõronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãne mãsu hankaltuwa.
بَلِ ٱتَّبَعَ ٱلَّذِینَ ظَلَمُوۤاْ أَهۡوَاۤءَهُم بِغَیۡرِ عِلۡمࣲۖ فَمَن یَهۡدِی مَنۡ أَضَلَّ ٱللَّهُۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِینَ ﴿٢٩﴾
Ã'aha! waɗanda suka yi zãunci sun bi son zũciyõyinsu, bã tãre da wani ilmi ba. To wãne ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar, kuma bã su da waɗansu mataimaka?
فَأَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّینِ حَنِیفࣰاۚ فِطۡرَتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِی فَطَرَ ٱلنَّاسَ عَلَیۡهَاۚ لَا تَبۡدِیلَ لِخَلۡقِ ٱللَّهِۚ ذَ ٰلِكَ ٱلدِّینُ ٱلۡقَیِّمُ وَلَـٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا یَعۡلَمُونَ ﴿٣٠﴾
Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini,* kanã mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutãne a kanta. Bãbu musanyãwa ga halittar Allah, wannan shĩ ne addini madaidaici kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
۞ مُنِیبِینَ إِلَیۡهِ وَٱتَّقُوهُ وَأَقِیمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَلَا تَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِینَ ﴿٣١﴾
Kunã mãsu mai da al'amari gare Shi, kuma ku bĩ Shi dataƙawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai.*
مِنَ ٱلَّذِینَ فَرَّقُواْ دِینَهُمۡ وَكَانُواْ شِیَعࣰاۖ كُلُّ حِزۡبِۭ بِمَا لَدَیۡهِمۡ فَرِحُونَ ﴿٣٢﴾
Wãtau waɗanda suka rarrabe addininsu kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kõwace ƙungiya tanã mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai.
وَإِذَا مَسَّ ٱلنَّاسَ ضُرࣱّ دَعَوۡاْ رَبَّهُم مُّنِیبِینَ إِلَیۡهِ ثُمَّ إِذَاۤ أَذَاقَهُم مِّنۡهُ رَحۡمَةً إِذَا فَرِیقࣱ مِّنۡهُم بِرَبِّهِمۡ یُشۡرِكُونَ ﴿٣٣﴾
Kuma idan cũta ta shãfi mutãne, sai su kirãyi Ubangijinsu, sunã mãsu mai da al'amari gare Shi, sa'an nan idan Ya ɗanɗana musu wata rahama daga gare Shi, sai gã wani ɓangare daga gare su sunã shirki da Ubangijinsu.
لِیَكۡفُرُواْ بِمَاۤ ءَاتَیۡنَـٰهُمۡۚ فَتَمَتَّعُواْ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ ﴿٣٤﴾
Dõmin su kãfirta dl abin da Muka bã su. To ku ji dãɗi kaɗan Sa'an nan zã ku, sani.
أَمۡ أَنزَلۡنَا عَلَیۡهِمۡ سُلۡطَـٰنࣰا فَهُوَ یَتَكَلَّمُ بِمَا كَانُواْ بِهِۦ یُشۡرِكُونَ ﴿٣٥﴾
Kõ Mun saukar da wani dalĩ li a gare su? Shi kuwa yanã magana da abin da suka kasance sunã shirkin da shi?
وَإِذَاۤ أَذَقۡنَا ٱلنَّاسَ رَحۡمَةࣰ فَرِحُواْ بِهَاۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَیِّئَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَیۡدِیهِمۡ إِذَا هُمۡ یَقۡنَطُونَ ﴿٣٦﴾
Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita kuma idan cũta ta sãme su, sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, sai gã su sunã yanke ƙauna,
أَوَلَمۡ یَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ یَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن یَشَاۤءُ وَیَقۡدِرُۚ إِنَّ فِی ذَ ٰلِكَ لَـَٔایَـٰتࣲ لِّقَوۡمࣲ یُؤۡمِنُونَ ﴿٣٧﴾
Shin, kuma ba su gani ba cẽwa Allah na shimfida arziki ga wanda Yake so kuma Yanã ƙuntatãwa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin ĩmãni.
فَـَٔاتِ ذَا ٱلۡقُرۡبَىٰ حَقَّهُۥ وَٱلۡمِسۡكِینَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِیلِۚ ذَ ٰلِكَ خَیۡرࣱ لِّلَّذِینَ یُرِیدُونَ وَجۡهَ ٱللَّهِۖ وَأُوْلَـٰۤىِٕكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ ﴿٣٨﴾
Sabõda haka ka bai wa zumu hakkinsa da miskĩnai da ɗan hanya, wannan shĩ ne alhẽri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan sũ ne mãsu sãmun babban rabo.
وَمَاۤ ءَاتَیۡتُم مِّن رِّبࣰا لِّیَرۡبُوَاْ فِیۤ أَمۡوَ ٰلِ ٱلنَّاسِ فَلَا یَرۡبُواْ عِندَ ٱللَّهِۖ وَمَاۤ ءَاتَیۡتُم مِّن زَكَوٰةࣲ تُرِیدُونَ وَجۡهَ ٱللَّهِ فَأُوْلَـٰۤىِٕكَ هُمُ ٱلۡمُضۡعِفُونَ ﴿٣٩﴾
Kuma abin da kuka bãyar na riba dõmin ya ƙãru a cikin dũkiyar mutãne to, bã zai ƙãru ba, a wurin Allah. Kuma abin da kuka bãyar na zakka, kanã nufin yardar Allah to (mãsu yin haka) waɗancan sũ ne mãsu ninkãwa (ga dũkiyarsu).
ٱللَّهُ ٱلَّذِی خَلَقَكُمۡ ثُمَّ رَزَقَكُمۡ ثُمَّ یُمِیتُكُمۡ ثُمَّ یُحۡیِیكُمۡۖ هَلۡ مِن شُرَكَاۤىِٕكُم مَّن یَفۡعَلُ مِن ذَ ٰلِكُم مِّن شَیۡءࣲۚ سُبۡحَـٰنَهُۥ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا یُشۡرِكُونَ ﴿٤٠﴾
Allah ne Wanda Ya halicce ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku, sa'an nan Ya rãyar da ku. Ashe, daga cikin abũbuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga waɗannan ahũbuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya ɗaukaka bisa ga abin da suke yi na shirki.
ظَهَرَ ٱلۡفَسَادُ فِی ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ بِمَا كَسَبَتۡ أَیۡدِی ٱلنَّاسِ لِیُذِیقَهُم بَعۡضَ ٱلَّذِی عَمِلُواْ لَعَلَّهُمۡ یَرۡجِعُونَ ﴿٤١﴾
¥arnã tã bayyana a cikin ƙasa da tẽku, sabõda abin da hannãyen mutãne suka aikata. Dõmin Allah Ya ɗanɗana musu sãshin abin da suka aikata, ɗammãninsu zã su kõmo.
قُلۡ سِیرُواْ فِی ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَیۡفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِینَ مِن قَبۡلُۚ كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّشۡرِكِینَ ﴿٤٢﴾
Ka ce: "Ku tafi a cikin ƙasã sa'an nan ku dũbi yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninku ta kasance. Mafi yawansu sun kasance mãsu yin shirka."
فَأَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّینِ ٱلۡقَیِّمِ مِن قَبۡلِ أَن یَأۡتِیَ یَوۡمࣱ لَّا مَرَدَّ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۖ یَوۡمَىِٕذࣲ یَصَّدَّعُونَ ﴿٤٣﴾
Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici a gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare Shi daga Allah, a rãnar nan mutãne sunã tsãgẽwa (su rabu biyu).
مَن كَفَرَ فَعَلَیۡهِ كُفۡرُهُۥۖ وَمَنۡ عَمِلَ صَـٰلِحࣰا فَلِأَنفُسِهِمۡ یَمۡهَدُونَ ﴿٤٤﴾
Wanda ya kãfirta, to, kãfircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, sabõda kansu suke yin shimfiɗa.
لِیَجۡزِیَ ٱلَّذِینَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ مِن فَضۡلِهِۦۤۚ إِنَّهُۥ لَا یُحِبُّ ٱلۡكَـٰفِرِینَ ﴿٤٥﴾
Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga falalarSa. Lalle Allah bã Ya son kafirai.
وَمِنۡ ءَایَـٰتِهِۦۤ أَن یُرۡسِلَ ٱلرِّیَاحَ مُبَشِّرَ ٰتࣲ وَلِیُذِیقَكُم مِّن رَّحۡمَتِهِۦ وَلِتَجۡرِیَ ٱلۡفُلۡكُ بِأَمۡرِهِۦ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ ﴿٤٦﴾
Kuma akwai daga ãyõyinSa, ya aika iskõki mãsu bãyar da bushãra kuma dõmin Ya ɗanɗana muku daga rahamarSa, kuma dõmin jirãgen ruwa su gudãna da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalar Sa, fãtanku zã ku gode.
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ رُسُلًا إِلَىٰ قَوۡمِهِمۡ فَجَاۤءُوهُم بِٱلۡبَیِّنَـٰتِ فَٱنتَقَمۡنَا مِنَ ٱلَّذِینَ أَجۡرَمُواْۖ وَكَانَ حَقًّا عَلَیۡنَا نَصۡرُ ٱلۡمُؤۡمِنِینَ ﴿٤٧﴾
Kuma lalle Mun aiki waɗansu Manzanni a gabãninka, zuwa ga mutãnensu sai suka je musu da hujjõji, bayyanannu, sa'an nan Muka azabtar da waɗanda suka yi laifi, kuma ya kasance tabbatacce taimakon mũminai wajibi ne a kan mu.
ٱللَّهُ ٱلَّذِی یُرۡسِلُ ٱلرِّیَـٰحَ فَتُثِیرُ سَحَابࣰا فَیَبۡسُطُهُۥ فِی ٱلسَّمَاۤءِ كَیۡفَ یَشَاۤءُ وَیَجۡعَلُهُۥ كِسَفࣰا فَتَرَى ٱلۡوَدۡقَ یَخۡرُجُ مِنۡ خِلَـٰلِهِۦۖ فَإِذَاۤ أَصَابَ بِهِۦ مَن یَشَاۤءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۤ إِذَا هُمۡ یَسۡتَبۡشِرُونَ ﴿٤٨﴾
Allah ne Wanda ke aika iskõki, sai su mõtsar da girgije, sa'an nan Ya shimfiɗa shi a cikin sama yadda Yake so, kuma Ya sanya shi wani ɓaɓɓake, sa'an nan ka ga ruwa na fita daga tsakãninsa. Sa'an nan idan Allah Ya sãmi waɗanda Ya so daga bãyinsa, Sai gã su suna bushãra da shi.
وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلِ أَن یُنَزَّلَ عَلَیۡهِم مِّن قَبۡلِهِۦ لَمُبۡلِسِینَ ﴿٤٩﴾
Kuma kõ da sun kasance a gabãnin a saukar da shi a kansu, kusa-kusa, sunã baƙin ciki hai bã su iya magana.
فَٱنظُرۡ إِلَىٰۤ ءَاثَـٰرِ رَحۡمَتِ ٱللَّهِ كَیۡفَ یُحۡیِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۤۚ إِنَّ ذَ ٰلِكَ لَمُحۡیِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَیۡءࣲ قَدِیرࣱ ﴿٥٠﴾
Sai ka dũbi alãmõmin rahamar Allah yadda Yake rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta. Lalle wannan (Mai wannan aiki), tabbas, Mai rãyar da halitta ne, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan kõme.
وَلَىِٕنۡ أَرۡسَلۡنَا رِیحࣰا فَرَأَوۡهُ مُصۡفَرࣰّا لَّظَلُّواْ مِنۢ بَعۡدِهِۦ یَكۡفُرُونَ ﴿٥١﴾
Kuma lalle idan Mun aika wata iska, suka ganta fatsifatsi, lalle zã su yini a bãyansa sunã kãfirta.
فَإِنَّكَ لَا تُسۡمِعُ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَلَا تُسۡمِعُ ٱلصُّمَّ ٱلدُّعَاۤءَ إِذَا وَلَّوۡاْ مُدۡبِرِینَ ﴿٥٢﴾
Sabõda haka, kai, bã ka jiyar da matattu kira, kuma bã ka jiyar da kurãme kira idan sun jũya bãya sunã gudu.
وَمَاۤ أَنتَ بِهَـٰدِ ٱلۡعُمۡیِ عَن ضَلَـٰلَتِهِمۡۖ إِن تُسۡمِعُ إِلَّا مَن یُؤۡمِنُ بِـَٔایَـٰتِنَا فَهُم مُّسۡلِمُونَ ﴿٥٣﴾
Kuma ba ka zamo mai shiryar da makãfi ba daga ɓatarsu, bã ka jiyarwa fãce wanda ke yin ĩmãni da ãyõyin Mu, watau sũ ne mãsu mĩƙa wuya, su sallama.
۞ ٱللَّهُ ٱلَّذِی خَلَقَكُم مِّن ضَعۡفࣲ ثُمَّ جَعَلَ مِنۢ بَعۡدِ ضَعۡفࣲ قُوَّةࣰ ثُمَّ جَعَلَ مِنۢ بَعۡدِ قُوَّةࣲ ضَعۡفࣰا وَشَیۡبَةࣰۚ یَخۡلُقُ مَا یَشَاۤءُۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِیمُ ٱلۡقَدِیرُ ﴿٥٤﴾
Allah ne Ya halitta ku daga rauni,* sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bãyan wani ƙarfi, Allah na halitta abin da Ya so, kuma Shĩ ne Mai ilmi, Mai ĩkon yi,
وَیَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ یُقۡسِمُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ مَا لَبِثُواْ غَیۡرَ سَاعَةࣲۚ كَذَ ٰلِكَ كَانُواْ یُؤۡفَكُونَ ﴿٥٥﴾
Kuma a rãnar da Sa'a* ke tsayuwa, mãsu laifi na rantsuwã: Ba su zauna a cikin kabari ba fãce sã'a guda. Kamar haka suka kasance anã karkatar da su.
وَقَالَ ٱلَّذِینَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ وَٱلۡإِیمَـٰنَ لَقَدۡ لَبِثۡتُمۡ فِی كِتَـٰبِ ٱللَّهِ إِلَىٰ یَوۡمِ ٱلۡبَعۡثِۖ فَهَـٰذَا یَوۡمُ ٱلۡبَعۡثِ وَلَـٰكِنَّكُمۡ كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ ﴿٥٦﴾
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi da ĩmãni suka ce: "Lalle, haƙĩƙa kun zauna a cikin Littãfin Allah, har zuwa rãnar tãyarwa, to, kuma wannan ita ce rãnar tãyarwar, kuma amma kũ, kun kasance* ba ku sani ba."
فَیَوۡمَىِٕذࣲ لَّا یَنفَعُ ٱلَّذِینَ ظَلَمُواْ مَعۡذِرَتُهُمۡ وَلَا هُمۡ یُسۡتَعۡتَبُونَ ﴿٥٧﴾
To, a rãnar da uzurin waɗanda suka yi zãlunci bã ya amfaninsu, kuma bã a neman yardarsu.
وَلَقَدۡ ضَرَبۡنَا لِلنَّاسِ فِی هَـٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ مِن كُلِّ مَثَلࣲۚ وَلَىِٕن جِئۡتَهُم بِـَٔایَةࣲ لَّیَقُولَنَّ ٱلَّذِینَ كَفَرُوۤاْ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا مُبۡطِلُونَ ﴿٥٨﴾
Kuma lalle tabbas Mun buga kõwane irin misãli ga mutãne a cikin wannan Alƙur'ãni, kuma lalle idan kã je musu da kõwace ãyã, lalle, waɗanda suka kãfirta zã su ce "Kũ, bã kõme kuke ba fãce mãsu barua."
كَذَ ٰلِكَ یَطۡبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلَّذِینَ لَا یَعۡلَمُونَ ﴿٥٩﴾
Kamar haka Allah Yake shãfe haske a kan zukãtan waɗanda ba su sani ba.