ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ فَاطِرِ ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ جَاعِلِ ٱلۡمَلَـٰۤىِٕكَةِ رُسُلًا أُوْلِیۤ أَجۡنِحَةࣲ مَّثۡنَىٰ وَثُلَـٰثَ وَرُبَـٰعَۚ یَزِیدُ فِی ٱلۡخَلۡقِ مَا یَشَاۤءُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَیۡءࣲ قَدِیرࣱ ﴿١﴾
Gõdiya ta tabbata ga Allah, Mai fãra halittar sammai da ƙasã, Mai sanya malã'iku manzanni mãsu fukãfukai, bibbiyu, da uku-uku da hurhuɗu. Yanã ƙãrãwar abin da Ya ke so a cikin halittar. Lalle Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme.
مَّا یَفۡتَحِ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ مِن رَّحۡمَةࣲ فَلَا مُمۡسِكَ لَهَاۖ وَمَا یُمۡسِكۡ فَلَا مُرۡسِلَ لَهُۥ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِیزُ ٱلۡحَكِیمُ ﴿٢﴾
Abin da Allah Ya buɗa wa mutãne daga rahama, to, bãbu mai riƙewa a gare shi, kuma abin da Ya riƙe, to, bãbu mai saki a gare shi, wanin Sa, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
یَـٰۤأَیُّهَا ٱلنَّاسُ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَیۡكُمۡۚ هَلۡ مِنۡ خَـٰلِقٍ غَیۡرُ ٱللَّهِ یَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَاۤءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَاۤ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ ﴿٣﴾
Yã kũ mutãne! Ku tuna ni'imar Allah a kanku. Shin, akwai wani mai halitta wanin Allah da zai azurta ku daga sama da, ƙasã? Bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?
وَإِن یُكَذِّبُوكَ فَقَدۡ كُذِّبَتۡ رُسُلࣱ مِّن قَبۡلِكَۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ ﴿٤﴾
Kuma idan sun ƙaryata ka, to, lalle, an ƙaryata waɗansu Manzanni a gabãninka, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura.
یَـٰۤأَیُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقࣱّۖ فَلَا تَغُرَّنَّكُمُ ٱلۡحَیَوٰةُ ٱلدُّنۡیَا وَلَا یَغُرَّنَّكُم بِٱللَّهِ ٱلۡغَرُورُ ﴿٥﴾
Yã kũ mutãne! Lalle wa'adin Allah gaskiya ne, sabõda haka kada rãyuwar dũniya ta rũɗar da ku, kuma kada marũɗi ya rũɗe ku game da Allah.
إِنَّ ٱلشَّیۡطَـٰنَ لَكُمۡ عَدُوࣱّ فَٱتَّخِذُوهُ عَدُوًّاۚ إِنَّمَا یَدۡعُواْ حِزۡبَهُۥ لِیَكُونُواْ مِنۡ أَصۡحَـٰبِ ٱلسَّعِیرِ ﴿٦﴾
Lalle Shaiɗan maƙiyi ne a gare ku, sai ku riƙe shi maƙiyi. Yanã kiran ƙungiyarsa kawai ne, dõmin su kasance 'yan sa'ir.
ٱلَّذِینَ كَفَرُواْ لَهُمۡ عَذَابࣱ شَدِیدࣱۖ وَٱلَّذِینَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ لَهُم مَّغۡفِرَةࣱ وَأَجۡرࣱ كَبِیرٌ ﴿٧﴾
Waɗanda suka kãfirta suna da azãba mai tsanani kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wata gãfara da sakamako mai girma.
أَفَمَن زُیِّنَ لَهُۥ سُوۤءُ عَمَلِهِۦ فَرَءَاهُ حَسَنࣰاۖ فَإِنَّ ٱللَّهَ یُضِلُّ مَن یَشَاۤءُ وَیَهۡدِی مَن یَشَاۤءُۖ فَلَا تَذۡهَبۡ نَفۡسُكَ عَلَیۡهِمۡ حَسَرَ ٰتٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِیمُۢ بِمَا یَصۡنَعُونَ ﴿٨﴾
Shin to, wanda aka ƙawãta masa aikinsa, har ya gan shi mai kyau (yanã daidai da waninsa)? Sabõda haka, lalle, Allah Yanã ɓatar da wanda Yake so, kuma Yanã shiryar da wanda Yake so, sabõda haka kada ranka ya halaka a kansu dômin baƙin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke sanã'antawa.
وَٱللَّهُ ٱلَّذِیۤ أَرۡسَلَ ٱلرِّیَـٰحَ فَتُثِیرُ سَحَابࣰا فَسُقۡنَـٰهُ إِلَىٰ بَلَدࣲ مَّیِّتࣲ فَأَحۡیَیۡنَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ كَذَ ٰلِكَ ٱلنُّشُورُ ﴿٩﴾
Kuma Allah ne Ya aika da iskõki har su mõtsar da girgije, sa'an nan Mu kõra shi zuwa ga gari matacce, sa'an nan Mu rãyar da ƙasã game da shi a bayan mutuwarta. Kamar wancan ne Tãshin ¡iyãma yake.
مَن كَانَ یُرِیدُ ٱلۡعِزَّةَ فَلِلَّهِ ٱلۡعِزَّةُ جَمِیعًاۚ إِلَیۡهِ یَصۡعَدُ ٱلۡكَلِمُ ٱلطَّیِّبُ وَٱلۡعَمَلُ ٱلصَّـٰلِحُ یَرۡفَعُهُۥۚ وَٱلَّذِینَ یَمۡكُرُونَ ٱلسَّیِّـَٔاتِ لَهُمۡ عَذَابࣱ شَدِیدࣱۖ وَمَكۡرُ أُوْلَـٰۤىِٕكَ هُوَ یَبُورُ ﴿١٠﴾
Wanda ya kasance yanã nẽman wata izza, to, Allah ne da izza gabã ɗaya. zuwa gare Shi magana mai dãɗi ke hawa, kuma aiki na ƙwarai Yanã ɗaukar ta Kuma waɗanda ke yin mãkircin mũnanan ayyuka, sunã da wata azãba mai tsanani, kuma mãkircin waɗannan yanã yin tasgaro.
وَٱللَّهُ خَلَقَكُم مِّن تُرَابࣲ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةࣲ ثُمَّ جَعَلَكُمۡ أَزۡوَ ٰجࣰاۚ وَمَا تَحۡمِلُ مِنۡ أُنثَىٰ وَلَا تَضَعُ إِلَّا بِعِلۡمِهِۦۚ وَمَا یُعَمَّرُ مِن مُّعَمَّرࣲ وَلَا یُنقَصُ مِنۡ عُمُرِهِۦۤ إِلَّا فِی كِتَـٰبٍۚ إِنَّ ذَ ٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ یَسِیرࣱ ﴿١١﴾
Kuma Allah ne Ya halitta ku daga turɓãya, sa'an nan daga ɗigon maniyyi, sa'an nan Ya sanya ku surkin maza da mãtã. Kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da saninSa, kuma bã zã a rãyar da wanda ake rãyarwa ba, kuma bã zã a rage tsawon ransa ba fãce yanã a cikin Littãfi. Lalle, wancan mai sauki ne ga Allah.
وَمَا یَسۡتَوِی ٱلۡبَحۡرَانِ هَـٰذَا عَذۡبࣱ فُرَاتࣱ سَاۤىِٕغࣱ شَرَابُهُۥ وَهَـٰذَا مِلۡحٌ أُجَاجࣱۖ وَمِن كُلࣲّ تَأۡكُلُونَ لَحۡمࣰا طَرِیࣰّا وَتَسۡتَخۡرِجُونَ حِلۡیَةࣰ تَلۡبَسُونَهَاۖ وَتَرَى ٱلۡفُلۡكَ فِیهِ مَوَاخِرَ لِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ ﴿١٢﴾
Kuma kõguna biyu ba su daidaita: Wannan mai ruwan dãɗi, mai zãƙi, mai sauƙin haɗiya kuma wannan mai ruwan gishiri mai zartsi, kuma daga kõwane, kunã cin wani nama sãbo, kuma kunã fitar da kawa wadda kuke tufantarta, kuma kanã ganin jirãge a cikinsa sunã mãsu gudãna, dõmin ku nẽmo daga falalar Sa, kuma tsammãninku zã ku dinga gõdẽwa.
یُولِجُ ٱلَّیۡلَ فِی ٱلنَّهَارِ وَیُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِی ٱلَّیۡلِ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلࣱّ یَجۡرِی لِأَجَلࣲ مُّسَمࣰّىۚ ذَ ٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ لَهُ ٱلۡمُلۡكُۚ وَٱلَّذِینَ تَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ مَا یَمۡلِكُونَ مِن قِطۡمِیرٍ ﴿١٣﴾
Yanã shigar da dare a cikin rãna, kuma Yanã shigar da rãna a cikin dare. Kuma Ya hõre rãnã da watã kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce Wannan Shĩ ne Allah, Ubangijinku, gare Shi mulki yake, kuma waɗanda kuke kira waninSa bã su mallakar kõ fãtar gurtsun dabĩno.
إِن تَدۡعُوهُمۡ لَا یَسۡمَعُواْ دُعَاۤءَكُمۡ وَلَوۡ سَمِعُواْ مَا ٱسۡتَجَابُواْ لَكُمۡۖ وَیَوۡمَ ٱلۡقِیَـٰمَةِ یَكۡفُرُونَ بِشِرۡكِكُمۡۚ وَلَا یُنَبِّئُكَ مِثۡلُ خَبِیرࣲ ﴿١٤﴾
Idan kun kira su, bã zã su ji kiranku ba, kuma kõ sun jiya, bã zã su karɓa muku ba, kuma a Rãnar ¡iyãma zã su kãfirce wa shirkinku, kuma bãbu mai bã ka lãbãri, kamar wanda ya sani.
۞ یَـٰۤأَیُّهَا ٱلنَّاسُ أَنتُمُ ٱلۡفُقَرَاۤءُ إِلَى ٱللَّهِۖ وَٱللَّهُ هُوَ ٱلۡغَنِیُّ ٱلۡحَمِیدُ ﴿١٥﴾
Yã kũ mutãne! Kũ ne mãsu bukãta zuwa ga Allah, kuma Allah, Shĩ ne Mawadãci, Gõdadde.
إِن یَشَأۡ یُذۡهِبۡكُمۡ وَیَأۡتِ بِخَلۡقࣲ جَدِیدࣲ ﴿١٦﴾
Idan Ya so, zai tafi da ku, kuma Ya zo da wata halitta sãbuwa.
وَلَا تَزِرُ وَازِرَةࣱ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ وَإِن تَدۡعُ مُثۡقَلَةٌ إِلَىٰ حِمۡلِهَا لَا یُحۡمَلۡ مِنۡهُ شَیۡءࣱ وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰۤۗ إِنَّمَا تُنذِرُ ٱلَّذِینَ یَخۡشَوۡنَ رَبَّهُم بِٱلۡغَیۡبِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَۚ وَمَن تَزَكَّىٰ فَإِنَّمَا یَتَزَكَّىٰ لِنَفۡسِهِۦۚ وَإِلَى ٱللَّهِ ٱلۡمَصِیرُ ﴿١٨﴾
Kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bai ɗaukar nauyin wani rai. Kuma idan ran da aka nauyaya wa kãya ya yi kira (ga wani mataimaki) zuwa ga kãyansa, bã zã a dauki kõme ba daga gare shi, kuma kõ dã (wanda ake kiran) yã kasance makusancin zumunta ne. Kanã gargaɗi kawai ne ga waɗanda ke tsoron Ubangijinsu a fake, kuma suka tsayar da salla. Kuma wanda ya tsarkake, to, yanã tsarkaka ne dõmin kansa. Kuma zuwa ga Allah kawai makõma take.
وَمَا یَسۡتَوِی ٱلۡأَحۡیَاۤءُ وَلَا ٱلۡأَمۡوَ ٰتُۚ إِنَّ ٱللَّهَ یُسۡمِعُ مَن یَشَاۤءُۖ وَمَاۤ أَنتَ بِمُسۡمِعࣲ مَّن فِی ٱلۡقُبُورِ ﴿٢٢﴾
Kuma rãyayyu bã su daidaita kuma matattu ba su daidaita. Lalle Allah Yanã jiyar da wa'azi ga wanda Ya so, kuma ba ka jiyar da waɗanda suke a cikin kaburbura.
إِنَّاۤ أَرۡسَلۡنَـٰكَ بِٱلۡحَقِّ بَشِیرࣰا وَنَذِیرࣰاۚ وَإِن مِّنۡ أُمَّةٍ إِلَّا خَلَا فِیهَا نَذِیرࣱ ﴿٢٤﴾
Lalle Mũ Mun aike ka da gaskiya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Kuma bãbu wata al'umma fãce wani mai gargaɗi yã shũɗe a cikinta.
وَإِن یُكَذِّبُوكَ فَقَدۡ كَذَّبَ ٱلَّذِینَ مِن قَبۡلِهِمۡ جَاۤءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَیِّنَـٰتِ وَبِٱلزُّبُرِ وَبِٱلۡكِتَـٰبِ ٱلۡمُنِیرِ ﴿٢٥﴾
Kuma idan sunã ƙaryata ka, to, haƙĩƙa, waɗanda suke a gabãninsu sun ƙaryata. Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji, kuma da takardu, kuma da Littafi mai haske.
ثُمَّ أَخَذۡتُ ٱلَّذِینَ كَفَرُواْۖ فَكَیۡفَ كَانَ نَكِیرِ ﴿٢٦﴾
Sa'an nan Na kãma waɗanda suka kãfirta. To, yãya musũ Na yake?
أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَاۤءِ مَاۤءࣰ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦ ثَمَرَ ٰتࣲ مُّخۡتَلِفًا أَلۡوَ ٰنُهَاۚ وَمِنَ ٱلۡجِبَالِ جُدَدُۢ بِیضࣱ وَحُمۡرࣱ مُّخۡتَلِفٌ أَلۡوَ ٰنُهَا وَغَرَابِیبُ سُودࣱ ﴿٢٧﴾
Ba ka gani ba, lalle Allah Ya saukar da ruwa daga sama? Sai Muka fitar, game da shi,'yã'yan itãce mãsu sãɓanin launuka kuma daga duwatsu akwai zane-zane, farfaru da jãjãye, mãsu sãɓanin launin, da mãsu launin baƙin ƙarfe, baƙãƙe.
وَمِنَ ٱلنَّاسِ وَٱلدَّوَاۤبِّ وَٱلۡأَنۡعَـٰمِ مُخۡتَلِفٌ أَلۡوَ ٰنُهُۥ كَذَ ٰلِكَۗ إِنَّمَا یَخۡشَى ٱللَّهَ مِنۡ عِبَادِهِ ٱلۡعُلَمَـٰۤؤُاْۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِیزٌ غَفُورٌ ﴿٢٨﴾
Kuma daga mutãne da dabbõbi da bisãshen gida, mãsu sãɓãnin launinsu kamar wancan. Malamai kawai ke tsõron Allah daga cikin bãyin Sa. Lalle, Allah, Mabuwãyi ne, Mai gãfara.
إِنَّ ٱلَّذِینَ یَتۡلُونَ كِتَـٰبَ ٱللَّهِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَـٰهُمۡ سِرࣰّا وَعَلَانِیَةࣰ یَرۡجُونَ تِجَـٰرَةࣰ لَّن تَبُورَ ﴿٢٩﴾
Lalle waɗanda ke karãtun Littãfin Allah* kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, sunã fãtan (sãmun) wani fatauci ne wanda bã ya yin tasgaro.
لِیُوَفِّیَهُمۡ أُجُورَهُمۡ وَیَزِیدَهُم مِّن فَضۡلِهِۦۤۚ إِنَّهُۥ غَفُورࣱ شَكُورࣱ ﴿٣٠﴾
Dõmin (Allah) zai cika musu sakamakonsu, kuma Ya ƙarã musu daga falalarSa. Lalle Shi Mai gãfara ne, Mai gõdiya.
وَٱلَّذِیۤ أَوۡحَیۡنَاۤ إِلَیۡكَ مِنَ ٱلۡكِتَـٰبِ هُوَ ٱلۡحَقُّ مُصَدِّقࣰا لِّمَا بَیۡنَ یَدَیۡهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِعِبَادِهِۦ لَخَبِیرُۢ بَصِیرࣱ ﴿٣١﴾
Kuma abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, daga Littãfi,
ثُمَّ أَوۡرَثۡنَا ٱلۡكِتَـٰبَ ٱلَّذِینَ ٱصۡطَفَیۡنَا مِنۡ عِبَادِنَاۖ فَمِنۡهُمۡ ظَالِمࣱ لِّنَفۡسِهِۦ وَمِنۡهُم مُّقۡتَصِدࣱ وَمِنۡهُمۡ سَابِقُۢ بِٱلۡخَیۡرَ ٰتِ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ ذَ ٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَضۡلُ ٱلۡكَبِیرُ ﴿٣٢﴾
Sa'an nan Mun gãdar da Littãfin, ga waɗanda Muka zãɓa daga bãyinMu, sa'an nan daga cikinsu, akwai mai zãlunci ga kansa, kuma daga cikinsu akwai mai tsakaitãwa, kuma daga cikinsu akwai mai tsẽrẽwa da ayyukan alhẽri da iznin Allah. Waccan ita ce falalar (Allah) mai girma.
جَنَّـٰتُ عَدۡنࣲ یَدۡخُلُونَهَا یُحَلَّوۡنَ فِیهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبࣲ وَلُؤۡلُؤࣰاۖ وَلِبَاسُهُمۡ فِیهَا حَرِیرࣱ ﴿٣٣﴾
Gidãjen Aljannar zamã sunã shigar su. Anã ƙawãce su a cikinsu, da ƙawã ta mundãye daga zĩnãriya da lu'ulu'u, kuma tufãfinsu, a cikinsu alharĩni ne.
وَقَالُواْ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِیۤ أَذۡهَبَ عَنَّا ٱلۡحَزَنَۖ إِنَّ رَبَّنَا لَغَفُورࣱ شَكُورٌ ﴿٣٤﴾
Kuma suka ce: "Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya tafiyar da baƙin ciki daga gare mu. Lalle Ubangijinmu, haƙĩƙa Mai gafarane, Mai godiya."
ٱلَّذِیۤ أَحَلَّنَا دَارَ ٱلۡمُقَامَةِ مِن فَضۡلِهِۦ لَا یَمَسُّنَا فِیهَا نَصَبࣱ وَلَا یَمَسُّنَا فِیهَا لُغُوبࣱ ﴿٣٥﴾
"Wanda Ya saukar da mu a gidan zamã, daga falalarSa, wata wahala bã ta shãfar mu a cikinsa, kuma wata kãsãwa bã ta shãfar mu a cikinsa."
وَٱلَّذِینَ كَفَرُواْ لَهُمۡ نَارُ جَهَنَّمَ لَا یُقۡضَىٰ عَلَیۡهِمۡ فَیَمُوتُواْ وَلَا یُخَفَّفُ عَنۡهُم مِّنۡ عَذَابِهَاۚ كَذَ ٰلِكَ نَجۡزِی كُلَّ كَفُورࣲ ﴿٣٦﴾
Kuma waɗanda suka kãfirta sunã da wutar Jahannama, bã a yin hukunci a kansu balle su mutu kuma bã a sauƙaƙa musu daga azãbarta. Kamar haka Muke sãka wa kõwane mai yawan kãfirci.
وَهُمۡ یَصۡطَرِخُونَ فِیهَا رَبَّنَاۤ أَخۡرِجۡنَا نَعۡمَلۡ صَـٰلِحًا غَیۡرَ ٱلَّذِی كُنَّا نَعۡمَلُۚ أَوَلَمۡ نُعَمِّرۡكُم مَّا یَتَذَكَّرُ فِیهِ مَن تَذَكَّرَ وَجَاۤءَكُمُ ٱلنَّذِیرُۖ فَذُوقُواْ فَمَا لِلظَّـٰلِمِینَ مِن نَّصِیرٍ ﴿٣٧﴾
Kuma sũ, sunã hargõwar nẽman ãgaji a cikinta. (Sunã cẽwa) "Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu, mu aikata aiki mai kyau, wanin wanda muka kasance munã aikatãwa." Ashe, kuma, ba Mu rãyar da ku ba, abin da mai tunãni zai iya yin tunãni a ciki, kuma mai gargaɗi yã jẽ muku? To, ku ɗanɗana, sabõda haka bãbu wani mataimaki, ga azzãlumai.
إِنَّ ٱللَّهَ عَـٰلِمُ غَیۡبِ ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ عَلِیمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ ﴿٣٨﴾
Lalle Allah ne Masanin gaibin sammai da ƙasã. Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake ainihin zukata.
هُوَ ٱلَّذِی جَعَلَكُمۡ خَلَـٰۤىِٕفَ فِی ٱلۡأَرۡضِۚ فَمَن كَفَرَ فَعَلَیۡهِ كُفۡرُهُۥۖ وَلَا یَزِیدُ ٱلۡكَـٰفِرِینَ كُفۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ إِلَّا مَقۡتࣰاۖ وَلَا یَزِیدُ ٱلۡكَـٰفِرِینَ كُفۡرُهُمۡ إِلَّا خَسَارࣰا ﴿٣٩﴾
Shĩ ne Wanda Ya sanya ku mãsu maye wa junã, a cikin ƙasã. To, wanda ya kãfirta, to, kãfircinsa yanã a kansa. Kuma kãfircin kãfirai bã ya kãra musu kõme fãce baƙin jini, kuma kãfircin kãfirai bã ya kãra musu kõme face hasãra.
قُلۡ أَرَءَیۡتُمۡ شُرَكَاۤءَكُمُ ٱلَّذِینَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِی مَاذَا خَلَقُواْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ لَهُمۡ شِرۡكࣱ فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ أَمۡ ءَاتَیۡنَـٰهُمۡ كِتَـٰبࣰا فَهُمۡ عَلَىٰ بَیِّنَتࣲ مِّنۡهُۚ بَلۡ إِن یَعِدُ ٱلظَّـٰلِمُونَ بَعۡضُهُم بَعۡضًا إِلَّا غُرُورًا ﴿٤٠﴾
Ka ce: "Shin, kun ga abũbuwan shirkinku, waɗanda kuke kira, wasun Allah? Ku nũna mini, mẽne ne suka halitta daga ƙasã? Kõ sunã da tãrayya ne a cikin sammai? Kõ kuma Mun bã su wani littãfi ne sabõda haka sunã a kan wata hujja ce daga gare shi? Ã'a, azzãlumai bã su yin wani wa'adi, sãshensu zuwa ga sãshe, fãce rũɗi."
۞ إِنَّ ٱللَّهَ یُمۡسِكُ ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ أَن تَزُولَاۚ وَلَىِٕن زَالَتَاۤ إِنۡ أَمۡسَكَهُمَا مِنۡ أَحَدࣲ مِّنۢ بَعۡدِهِۦۤۚ إِنَّهُۥ كَانَ حَلِیمًا غَفُورࣰا ﴿٤١﴾
Lalle Allah Yanã riƙe sammai da ƙasã dõmin kada su gushe. Kuma haƙĩƙa, idan sun gushe, bãbu wani baicin Sa da zai riƙe su. Lalle Shi Yã kasance Mai haƙuri, Mai gãfara.
وَأَقۡسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهۡدَ أَیۡمَـٰنِهِمۡ لَىِٕن جَاۤءَهُمۡ نَذِیرࣱ لَّیَكُونُنَّ أَهۡدَىٰ مِنۡ إِحۡدَى ٱلۡأُمَمِۖ فَلَمَّا جَاۤءَهُمۡ نَذِیرࣱ مَّا زَادَهُمۡ إِلَّا نُفُورًا ﴿٤٢﴾
Kuma suka* yi rantsuwa da Allah, mafi nauyin rantsuwarsu, "Lalle, idan wani mai gargaɗi ya zo musu tabbas zã su kasance mafi shiryuwa, daga ɗayan al'ummõmi." To, a lõkacin da mai gargaɗi ya jẽ musu, bai ƙarã su da kõme ba fãce gudu.
ٱسۡتِكۡبَارࣰا فِی ٱلۡأَرۡضِ وَمَكۡرَ ٱلسَّیِّىِٕۚ وَلَا یَحِیقُ ٱلۡمَكۡرُ ٱلسَّیِّئُ إِلَّا بِأَهۡلِهِۦۚ فَهَلۡ یَنظُرُونَ إِلَّا سُنَّتَ ٱلۡأَوَّلِینَۚ فَلَن تَجِدَ لِسُنَّتِ ٱللَّهِ تَبۡدِیلࣰاۖ وَلَن تَجِدَ لِسُنَّتِ ٱللَّهِ تَحۡوِیلًا ﴿٤٣﴾
Dõmin nũna girman kai a cikin ƙasã da mãkircin cũta. Kuma mãkirci na cũta bã ya fãdãwa fãce a kan mutãnensa. To shin sunã jiran (wani abu ne) fãce dai hanyar (kãfiran) farko. To, bã zã ka sãmi musanya ba ga hanyar Allah. Kuma bã zã ka sãmi jũyarwa ba ga hanyar Allah.
أَوَلَمۡ یَسِیرُواْ فِی ٱلۡأَرۡضِ فَیَنظُرُواْ كَیۡفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِینَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَكَانُوۤاْ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةࣰۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِیُعۡجِزَهُۥ مِن شَیۡءࣲ فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَلَا فِی ٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَلِیمࣰا قَدِیرࣰا ﴿٤٤﴾
Ashe, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba yadda ãƙibar waɗannan da suke a gabãninsu ta kasance? Alhãli kuwa sun kasance mafĩfĩta ƙarfi daga gare su? Kuma Allah bai kasance wani abu nã iya rinjãyar Sa ba, a cikin sammai, kuma haka a cikin kaƙã. Lalle Shi ne Ya kasance Masani, Mai ĩkon yi.
وَلَوۡ یُؤَاخِذُ ٱللَّهُ ٱلنَّاسَ بِمَا كَسَبُواْ مَا تَرَكَ عَلَىٰ ظَهۡرِهَا مِن دَاۤبَّةࣲ وَلَـٰكِن یُؤَخِّرُهُمۡ إِلَىٰۤ أَجَلࣲ مُّسَمࣰّىۖ فَإِذَا جَاۤءَ أَجَلُهُمۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِعِبَادِهِۦ بَصِیرَۢا ﴿٤٥﴾
Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne sabõda abin da suka aikata, dã bai bar wata dabba ba a kanta (kasã). Amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajalin da aka ambatã. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, to, lalle Allah yã kasance Mai gani ga bãyin Sa.