Surah At-Taghabun (Mutual Loss & Gain)

Listen

Hausa

Surah At-Taghabun (Mutual Loss & Gain) - Aya count 18

یُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰ⁠تِ وَمَا فِی ٱلۡأَرۡضِۖ لَهُ ٱلۡمُلۡكُ وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَیۡءࣲ قَدِیرٌ ﴿١﴾

Abin da yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasã sunã tasbĩhi ga Allah. Gare Shi mulki yake, kuma gare Shi gõdiya take. Kuma Shi, a kan kõme, Mai ikon yi ne.


Arabic explanations of the Qur’an:

هُوَ ٱلَّذِی خَلَقَكُمۡ فَمِنكُمۡ كَافِرࣱ وَمِنكُم مُّؤۡمِنࣱۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِیرٌ ﴿٢﴾

Shĩ ne wanda Ya halitta ku. Sa'an nan daga gare ku akwai kãfiri kuma daga gare ku akwai mũmini. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.


Arabic explanations of the Qur’an:

خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَ ٰ⁠تِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّ وَصَوَّرَكُمۡ فَأَحۡسَنَ صُوَرَكُمۡۖ وَإِلَیۡهِ ٱلۡمَصِیرُ ﴿٣﴾

Ya halitta sammai da ƙasã da abin da yake hakkin Sa. Kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku. Kuma zuwa gare Shi makõma take.


Arabic explanations of the Qur’an:

یَعۡلَمُ مَا فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰ⁠تِ وَٱلۡأَرۡضِ وَیَعۡلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعۡلِنُونَۚ وَٱللَّهُ عَلِیمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ ﴿٤﴾

Yanã sanin abin da ke a cikin sammai da ƙassai. Kuma Yanã sanin abin da kuke bõyẽwa da abin da kuke bayyanãwa. Kuma Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.


Arabic explanations of the Qur’an:

أَلَمۡ یَأۡتِكُمۡ نَبَؤُاْ ٱلَّذِینَ كَفَرُواْ مِن قَبۡلُ فَذَاقُواْ وَبَالَ أَمۡرِهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِیمࣱ ﴿٥﴾

Shin, babban lãbãri bai je muku ba na waɗanda suka kãfirta daga gabãni, sai suka ɗanɗani uƙũbar al'amarinsu kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi?


Arabic explanations of the Qur’an:

ذَ ٰ⁠لِكَ بِأَنَّهُۥ كَانَت تَّأۡتِیهِمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَیِّنَـٰتِ فَقَالُوۤاْ أَبَشَرࣱ یَهۡدُونَنَا فَكَفَرُواْ وَتَوَلَّواْۖ وَّٱسۡتَغۡنَى ٱللَّهُۚ وَٱللَّهُ غَنِیٌّ حَمِیدࣱ ﴿٦﴾

Wancan sabõda lalle su Manzanninsu sun kasance sunã jẽ musu da hujjõji bayyanannu, sai suka ce: "Ashe, wasu mutane za su shiryar da mũ?" Sai suka kãfirta kuma suka jũya bãya, kuma Allah Ya wadãtu (daga gare su). Kuma Allah wadãtacce ne, Gõdadde.


Arabic explanations of the Qur’an:

زَعَمَ ٱلَّذِینَ كَفَرُوۤاْ أَن لَّن یُبۡعَثُواْۚ قُلۡ بَلَىٰ وَرَبِّی لَتُبۡعَثُنَّ ثُمَّ لَتُنَبَّؤُنَّ بِمَا عَمِلۡتُمۡۚ وَذَ ٰ⁠لِكَ عَلَى ٱللَّهِ یَسِیرࣱ ﴿٧﴾

Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: "Ni, inã rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi ne."


Arabic explanations of the Qur’an:

فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَٱلنُّورِ ٱلَّذِیۤ أَنزَلۡنَاۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِیرࣱ ﴿٨﴾

Sabõda haka ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa da hasken nan da Muka saukar. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai labartawa ne.


Arabic explanations of the Qur’an:

یَوۡمَ یَجۡمَعُكُمۡ لِیَوۡمِ ٱلۡجَمۡعِۖ ذَ ٰ⁠لِكَ یَوۡمُ ٱلتَّغَابُنِۗ وَمَن یُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ وَیَعۡمَلۡ صَـٰلِحࣰا یُكَفِّرۡ عَنۡهُ سَیِّـَٔاتِهِۦ وَیُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتࣲ تَجۡرِی مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَـٰرُ خَـٰلِدِینَ فِیهَاۤ أَبَدࣰاۚ ذَ ٰ⁠لِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِیمُ ﴿٩﴾

A rãnar da Yake tattara ku dõmin rãnar tãruwa. Wancan ne rãnar kãmunga. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai girma.


Arabic explanations of the Qur’an:

وَٱلَّذِینَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔایَـٰتِنَاۤ أُوْلَـٰۤىِٕكَ أَصۡحَـٰبُ ٱلنَّارِ خَـٰلِدِینَ فِیهَاۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِیرُ ﴿١٠﴾

Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ayõyin Mu, waɗannan sũne'yan wuta, sunã madawwama a cikinta. Kuma tir da makõma, ita.


Arabic explanations of the Qur’an:

مَاۤ أَصَابَ مِن مُّصِیبَةٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَمَن یُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ یَهۡدِ قَلۡبَهُۥۚ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَیۡءٍ عَلِیمࣱ ﴿١١﴾

Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne.


Arabic explanations of the Qur’an:

وَأَطِیعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِیعُواْ ٱلرَّسُولَۚ فَإِن تَوَلَّیۡتُمۡ فَإِنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا ٱلۡبَلَـٰغُ ٱلۡمُبِینُ ﴿١٢﴾

Kuma ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo. Sa'an nan idan kun jũya bãya, to, abin sani kawai, akwai iyarwa bayyananna a kan Manzon Mu.


Arabic explanations of the Qur’an:

ٱللَّهُ لَاۤ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡیَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ﴿١٣﴾

Allah bãbu wani abin bauta wa fãce Shi. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara.


Arabic explanations of the Qur’an:

یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوۤاْ إِنَّ مِنۡ أَزۡوَ ٰ⁠جِكُمۡ وَأَوۡلَـٰدِكُمۡ عَدُوࣰّا لَّكُمۡ فَٱحۡذَرُوهُمۡۚ وَإِن تَعۡفُواْ وَتَصۡفَحُواْ وَتَغۡفِرُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورࣱ رَّحِیمٌ ﴿١٤﴾

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi* a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

* Maƙiyi, shĩ ne mai hana mutumin da yake ƙiyayya da shi wani alheri ya sadu da shi. Idan son dũkiya kõ mãta kõ ɗiya ya hana mutum yin sadaka kõ fita zuwa jihãdji, to dũkiyar da mãtan da ɗiyan sun zama maƙiyansa ke nan.


Arabic explanations of the Qur’an:

إِنَّمَاۤ أَمۡوَ ٰ⁠لُكُمۡ وَأَوۡلَـٰدُكُمۡ فِتۡنَةࣱۚ وَٱللَّهُ عِندَهُۥۤ أَجۡرٌ عَظِیمࣱ ﴿١٥﴾

Dũkiyõyinku da ɗiyanku fitina* ɗai ne. Kuma Allah, a wurin Sa akwai wani sakamako mai girma.

* Fitina, ita ce duk abin da zai cũci mutum ta hanyar da yake amincewa, cũtar ta dũniya ce kõ ta Lãhira. Cũtar Lãhira ta fi tsanani sabõda girman hasãrar da ke a cikinta.


Arabic explanations of the Qur’an:

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُمۡ وَٱسۡمَعُواْ وَأَطِیعُواْ وَأَنفِقُواْ خَیۡرࣰا لِّأَنفُسِكُمۡۗ وَمَن یُوقَ شُحَّ نَفۡسِهِۦ فَأُوْلَـٰۤىِٕكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ ﴿١٦﴾

Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma ku yi ɗã'ã, kuma ku ciyar, ya fi zama alhẽri gare ku. Kuma wandaya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.


Arabic explanations of the Qur’an:

إِن تُقۡرِضُواْ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنࣰا یُضَـٰعِفۡهُ لَكُمۡ وَیَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ شَكُورٌ حَلِیمٌ ﴿١٧﴾

Idan kun bai wa Allah rance, rance mai kyau, (Allah) zai ninka shi a gare ku kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai yawan gõdiya ne, Mai haƙuri.


Arabic explanations of the Qur’an:

عَـٰلِمُ ٱلۡغَیۡبِ وَٱلشَّهَـٰدَةِ ٱلۡعَزِیزُ ٱلۡحَكِیمُ ﴿١٨﴾

Shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwayi, Mai hikima.


Arabic explanations of the Qur’an: