This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah Al-Haaqqah (The Inevitable).
ٱلۡحَاۤقَّةُ
﴿١﴾
Kiran gaskiya!(1)
Tafseer:
مَا ٱلۡحَاۤقَّةُ
﴿٢﴾
Mẽne ne kiran gaskiya?(2)
Tafseer:
وَمَاۤ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡحَاۤقَّةُ
﴿٣﴾
Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?(3)
Tafseer:
كَذَّبَتۡ ثَمُودُ وَعَادُۢ بِٱلۡقَارِعَةِ
﴿٤﴾
Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!(4)
Tafseer:
فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهۡلِكُواْ بِٱلطَّاغِیَةِ
﴿٥﴾
To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.(5)
Tafseer:
وَأَمَّا عَادࣱ فَأُهۡلِكُواْ بِرِیحࣲ صَرۡصَرٍ عَاتِیَةࣲ
﴿٦﴾
Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.(6)
Tafseer:
سَخَّرَهَا عَلَیۡهِمۡ سَبۡعَ لَیَالࣲ وَثَمَـٰنِیَةَ أَیَّامٍ حُسُومࣰاۖ فَتَرَى ٱلۡقَوۡمَ فِیهَا صَرۡعَىٰ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٍ خَاوِیَةࣲ
﴿٧﴾
(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.(7)
Tafseer:
فَهَلۡ تَرَىٰ لَهُم مِّنۢ بَاقِیَةࣲ
﴿٨﴾
To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?(8)
Tafseer:
وَجَاۤءَ فِرۡعَوۡنُ وَمَن قَبۡلَهُۥ وَٱلۡمُؤۡتَفِكَـٰتُ بِٱلۡخَاطِئَةِ
﴿٩﴾
Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi.(9)
Tafseer:
فَعَصَوۡاْ رَسُولَ رَبِّهِمۡ فَأَخَذَهُمۡ أَخۡذَةࣰ رَّابِیَةً
﴿١٠﴾
Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani).(10)
Tafseer:
إِنَّا لَمَّا طَغَا ٱلۡمَاۤءُ حَمَلۡنَـٰكُمۡ فِی ٱلۡجَارِیَةِ
﴿١١﴾
Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan.(11)
Tafseer:
لِنَجۡعَلَهَا لَكُمۡ تَذۡكِرَةࣰ وَتَعِیَهَاۤ أُذُنࣱ وَ ٰعِیَةࣱ
﴿١٢﴾
Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi).(12)
Tafseer:
فَإِذَا نُفِخَ فِی ٱلصُّورِ نَفۡخَةࣱ وَ ٰحِدَةࣱ
﴿١٣﴾
To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.(13)
Tafseer:
وَحُمِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَٱلۡجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةࣰ وَ ٰحِدَةࣰ
﴿١٤﴾
Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.(14)
Tafseer:
فَیَوۡمَىِٕذࣲ وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ
﴿١٥﴾
A ran nan, mai aukuwa zã ta auku.(15)
Tafseer:
وَٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَاۤءُ فَهِیَ یَوۡمَىِٕذࣲ وَاهِیَةࣱ
﴿١٦﴾
Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.(16)
Tafseer:
وَٱلۡمَلَكُ عَلَىٰۤ أَرۡجَاۤىِٕهَاۚ وَیَحۡمِلُ عَرۡشَ رَبِّكَ فَوۡقَهُمۡ یَوۡمَىِٕذࣲ ثَمَـٰنِیَةࣱ
﴿١٧﴾
Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.(17)
Tafseer:
یَوۡمَىِٕذࣲ تُعۡرَضُونَ لَا تَخۡفَىٰ مِنكُمۡ خَافِیَةࣱ
﴿١٨﴾
A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa.(18)
Tafseer:
فَأَمَّا مَنۡ أُوتِیَ كِتَـٰبَهُۥ بِیَمِینِهِۦ فَیَقُولُ هَاۤؤُمُ ٱقۡرَءُواْ كِتَـٰبِیَهۡ
﴿١٩﴾
To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina."(19)
Tafseer:
إِنِّی ظَنَنتُ أَنِّی مُلَـٰقٍ حِسَابِیَهۡ
﴿٢٠﴾
"Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne."(20)
Tafseer:
فَهُوَ فِی عِیشَةࣲ رَّاضِیَةࣲ
﴿٢١﴾
Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda.(21)
Tafseer:
فِی جَنَّةٍ عَالِیَةࣲ
﴿٢٢﴾
A cikin Aljanna maɗaukakiya.(22)
Tafseer:
قُطُوفُهَا دَانِیَةࣱ
﴿٢٣﴾
Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),(23)
Tafseer:
كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِیۤـَٔۢا بِمَاۤ أَسۡلَفۡتُمۡ فِی ٱلۡأَیَّامِ ٱلۡخَالِیَةِ
﴿٢٤﴾
(Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige."(24)
Tafseer:
وَأَمَّا مَنۡ أُوتِیَ كِتَـٰبَهُۥ بِشِمَالِهِۦ فَیَقُولُ یَـٰلَیۡتَنِی لَمۡ أُوتَ كِتَـٰبِیَهۡ
﴿٢٥﴾
Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!"(25)
Tafseer:
وَلَمۡ أَدۡرِ مَا حِسَابِیَهۡ
﴿٢٦﴾
"Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!"(26)
Tafseer:
یَـٰلَیۡتَهَا كَانَتِ ٱلۡقَاضِیَةَ
﴿٢٧﴾
"In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!(27)
Tafseer:
مَاۤ أَغۡنَىٰ عَنِّی مَالِیَهۡۜ
﴿٢٨﴾
"Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!"(28)
Tafseer:
هَلَكَ عَنِّی سُلۡطَـٰنِیَهۡ
﴿٢٩﴾
"Ĩkona ya ɓace mini!"(29)
Tafseer:
خُذُوهُ فَغُلُّوهُ
﴿٣٠﴾
(Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi."(30)
Tafseer:
ثُمَّ ٱلۡجَحِیمَ صَلُّوهُ
﴿٣١﴾
"Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi."(31)
Tafseer:
ثُمَّ فِی سِلۡسِلَةࣲ ذَرۡعُهَا سَبۡعُونَ ذِرَاعࣰا فَٱسۡلُكُوهُ
﴿٣٢﴾
"Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi."(32)
Tafseer:
إِنَّهُۥ كَانَ لَا یُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ ٱلۡعَظِیمِ
﴿٣٣﴾
"Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!"(33)
Tafseer:
وَلَا یَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِینِ
﴿٣٤﴾
"Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!"(34)
Tafseer:
فَلَیۡسَ لَهُ ٱلۡیَوۡمَ هَـٰهُنَا حَمِیمࣱ
﴿٣٥﴾
"Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi."(35)
Tafseer:
وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنۡ غِسۡلِینࣲ
﴿٣٦﴾
"Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn."(36)
Tafseer:
لَّا یَأۡكُلُهُۥۤ إِلَّا ٱلۡخَـٰطِـُٔونَ
﴿٣٧﴾
"Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci."(37)
Tafseer:
فَلَاۤ أُقۡسِمُ بِمَا تُبۡصِرُونَ
﴿٣٨﴾
To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,(38)
Tafseer:
وَمَا لَا تُبۡصِرُونَ
﴿٣٩﴾
Da abin da bã ku iya gani.(39)
Tafseer:
إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولࣲ كَرِیمࣲ
﴿٤٠﴾
Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.(40)
Tafseer:
وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَاعِرࣲۚ قَلِیلࣰا مَّا تُؤۡمِنُونَ
﴿٤١﴾
Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.(41)
Tafseer:
وَلَا بِقَوۡلِ كَاهِنࣲۚ قَلِیلࣰا مَّا تَذَكَّرُونَ
﴿٤٢﴾
Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.(42)
Tafseer:
تَنزِیلࣱ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَـٰلَمِینَ
﴿٤٣﴾
Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.(43)
Tafseer:
وَلَوۡ تَقَوَّلَ عَلَیۡنَا بَعۡضَ ٱلۡأَقَاوِیلِ
﴿٤٤﴾
Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.(44)
Tafseer:
لَأَخَذۡنَا مِنۡهُ بِٱلۡیَمِینِ
﴿٤٥﴾
Dã Mun kãma shi da dãma.(45)
Tafseer:
ثُمَّ لَقَطَعۡنَا مِنۡهُ ٱلۡوَتِینَ
﴿٤٦﴾
sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.(46)
Tafseer:
فَمَا مِنكُم مِّنۡ أَحَدٍ عَنۡهُ حَـٰجِزِینَ
﴿٤٧﴾
Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbar Mu) daga gare shi.(47)
Tafseer:
وَإِنَّهُۥ لَتَذۡكِرَةࣱ لِّلۡمُتَّقِینَ
﴿٤٨﴾
Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.(48)
Tafseer:
وَإِنَّا لَنَعۡلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِینَ
﴿٤٩﴾
Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.(49)
Tafseer:
وَإِنَّهُۥ لَحَسۡرَةٌ عَلَى ٱلۡكَـٰفِرِینَ
﴿٥٠﴾
Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.(50)
Tafseer:
وَإِنَّهُۥ لَحَقُّ ٱلۡیَقِینِ
﴿٥١﴾
Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙini.(51)
Tafseer:
فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِیمِ
﴿٥٢﴾
Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.(52)
Tafseer: