This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah At-Takwir (The Overthrowing).
إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ
﴿١﴾
Idan rãna aka shafe haskenta(1)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتۡ
﴿٢﴾
Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).(2)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ سُیِّرَتۡ
﴿٣﴾
Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.(3)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلۡعِشَارُ عُطِّلَتۡ
﴿٤﴾
Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna* aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
* Rãƙuma mãsu ciki ɗan wata gõma.
(4)Tafseer:
وَإِذَا ٱلۡوُحُوشُ حُشِرَتۡ
﴿٥﴾
Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.(5)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ سُجِّرَتۡ
﴿٦﴾
Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.(6)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتۡ
﴿٧﴾
Kuma idan rãyuka aka haɗa* su da jikunkunansu.
* Ko kuma, aka haɗa kõwane mutum da irin mutãnensa a Aljanna ko a wuta.
(7)Tafseer:
وَإِذَا ٱلۡمَوۡءُۥدَةُ سُىِٕلَتۡ
﴿٨﴾
Kuma idan wadda aka turbuɗe* ta da rai aka tambaye ta.
* A cikin zãmanin jahiliyya Lãrabãwa bã su son a haifa musu 'ya'ya mãta dõmin haka har sukan turbuɗe 'ya'yansu dõmin kada su yi abin kunya ko kuma su talauce wajen yi musu aure.
(8)Tafseer:
بِأَیِّ ذَنۢبࣲ قُتِلَتۡ
﴿٩﴾
"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"(9)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتۡ
﴿١٠﴾
Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).(10)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلسَّمَاۤءُ كُشِطَتۡ
﴿١١﴾
Kuma idan sama aka fẽɗe ta.(11)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلۡجَحِیمُ سُعِّرَتۡ
﴿١٢﴾
Kuma idan Jahĩm aka hũra ta(12)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلۡجَنَّةُ أُزۡلِفَتۡ
﴿١٣﴾
Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.(13)
Tafseer:
عَلِمَتۡ نَفۡسࣱ مَّاۤ أَحۡضَرَتۡ
﴿١٤﴾
Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).(14)
Tafseer:
فَلَاۤ أُقۡسِمُ بِٱلۡخُنَّسِ
﴿١٥﴾
To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã* ba.
* Masu tafiya suna kõmawa bãya.
(15)Tafseer:
ٱلۡجَوَارِ ٱلۡكُنَّسِ
﴿١٦﴾
Mãsu gudu suna ɓũya.(16)
Tafseer:
وَٱلَّیۡلِ إِذَا عَسۡعَسَ
﴿١٧﴾
Da dare idan ya bãyar da bãya.(17)
Tafseer:
وَٱلصُّبۡحِ إِذَا تَنَفَّسَ
﴿١٨﴾
Da sãfiya idan ta yi lumfashi.(18)
Tafseer:
إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولࣲ كَرِیمࣲ
﴿١٩﴾
Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.(19)
Tafseer:
ذِی قُوَّةٍ عِندَ ذِی ٱلۡعَرۡشِ مَكِینࣲ
﴿٢٠﴾
Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.(20)
Tafseer:
مُّطَاعࣲ ثَمَّ أَمِینࣲ
﴿٢١﴾
Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.(21)
Tafseer:
وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجۡنُونࣲ
﴿٢٢﴾
Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.(22)
Tafseer:
وَلَقَدۡ رَءَاهُ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡمُبِینِ
﴿٢٣﴾
Kuma lalle ne, yã gan shi* a cikin sararin sama mabayyani.
* Annabi ya ga Mala'ika Jibirilu ya san shi. Sabõda haka wani aljani bã zai yi kama da shi ba balle ya kãwo masa ƙarya.
(23)Tafseer:
وَمَا هُوَ عَلَى ٱلۡغَیۡبِ بِضَنِینࣲ
﴿٢٤﴾
Kuma shi, ga gaibi* bã mai rowa ba ne.
* Ma'anar gaibi a nan, ilmin da Allah Ya aiko Jibirilu da shi zuwa ga Annabi Annabi ba ya ɓõye shi daga mutãne. Ga wata ƙira'a, wanda ake tuhuma, wãto ba a tuhumar Annabi, ga gaibin da ya faɗi cewa daga Allah yake, wato Alƙur'ãni duka gaskiya ne.
(24)Tafseer:
وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَیۡطَـٰنࣲ رَّجِیمࣲ
﴿٢٥﴾
Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.(25)
Tafseer:
فَأَیۡنَ تَذۡهَبُونَ
﴿٢٦﴾
Shin, a inã zã ku tafi?(26)
Tafseer:
إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرࣱ لِّلۡعَـٰلَمِینَ
﴿٢٧﴾
Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.(27)
Tafseer:
لِمَن شَاۤءَ مِنكُمۡ أَن یَسۡتَقِیمَ
﴿٢٨﴾
Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.(28)
Tafseer:
وَمَا تَشَاۤءُونَ إِلَّاۤ أَن یَشَاۤءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَـٰلَمِینَ
﴿٢٩﴾
Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.(29)
Tafseer: