This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud).
وَیۡلࣱ لِّلۡمُطَفِّفِینَ
﴿١﴾
Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.(1)
Tafseer:
ٱلَّذِینَ إِذَا ٱكۡتَالُواْ عَلَى ٱلنَّاسِ یَسۡتَوۡفُونَ
﴿٢﴾
Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.(2)
Tafseer:
وَإِذَا كَالُوهُمۡ أَو وَّزَنُوهُمۡ یُخۡسِرُونَ
﴿٣﴾
Kuma idan sun auna musu da zakka* ko da sikẽli, suna ragẽwa
* Mũdu.
(3)Tafseer:
أَلَا یَظُنُّ أُوْلَـٰۤىِٕكَ أَنَّهُم مَّبۡعُوثُونَ
﴿٤﴾
Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?(4)
Tafseer:
لِیَوۡمٍ عَظِیمࣲ
﴿٥﴾
Domin yini mai girma.(5)
Tafseer:
یَوۡمَ یَقُومُ ٱلنَّاسُ لِرَبِّ ٱلۡعَـٰلَمِینَ
﴿٦﴾
Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?(6)
Tafseer:
كَلَّاۤ إِنَّ كِتَـٰبَ ٱلۡفُجَّارِ لَفِی سِجِّینࣲ
﴿٧﴾
Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.(7)
Tafseer:
وَمَاۤ أَدۡرَىٰكَ مَا سِجِّینࣱ
﴿٨﴾
Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?(8)
Tafseer:
كِتَـٰبࣱ مَّرۡقُومࣱ
﴿٩﴾
Wani ittãfi ne rubũtacce.(9)
Tafseer:
وَیۡلࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِینَ
﴿١٠﴾
Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.(10)
Tafseer:
ٱلَّذِینَ یُكَذِّبُونَ بِیَوۡمِ ٱلدِّینِ
﴿١١﴾
Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.(11)
Tafseer:
وَمَا یُكَذِّبُ بِهِۦۤ إِلَّا كُلُّ مُعۡتَدٍ أَثِیمٍ
﴿١٢﴾
Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.(12)
Tafseer:
إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَیۡهِ ءَایَـٰتُنَا قَالَ أَسَـٰطِیرُ ٱلۡأَوَّلِینَ
﴿١٣﴾
Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.(13)
Tafseer:
كَلَّاۖ بَلۡۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُواْ یَكۡسِبُونَ
﴿١٤﴾
A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.(14)
Tafseer:
كَلَّاۤ إِنَّهُمۡ عَن رَّبِّهِمۡ یَوۡمَىِٕذࣲ لَّمَحۡجُوبُونَ
﴿١٥﴾
A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.(15)
Tafseer:
ثُمَّ إِنَّهُمۡ لَصَالُواْ ٱلۡجَحِیمِ
﴿١٦﴾
Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.(16)
Tafseer:
ثُمَّ یُقَالُ هَـٰذَا ٱلَّذِی كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
﴿١٧﴾
Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."(17)
Tafseer:
كَلَّاۤ إِنَّ كِتَـٰبَ ٱلۡأَبۡرَارِ لَفِی عِلِّیِّینَ
﴿١٨﴾
A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?(18)
Tafseer:
وَمَاۤ أَدۡرَىٰكَ مَا عِلِّیُّونَ
﴿١٩﴾
Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?(19)
Tafseer:
كِتَـٰبࣱ مَّرۡقُومࣱ
﴿٢٠﴾
Wani littãfi ne rubũtacce.(20)
Tafseer:
یَشۡهَدُهُ ٱلۡمُقَرَّبُونَ
﴿٢١﴾
Muƙarrabai* suke halarta shi.
* Malã'iku masu daraja.
(21)Tafseer:
إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِی نَعِیمٍ
﴿٢٢﴾
Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.(22)
Tafseer:
عَلَى ٱلۡأَرَاۤىِٕكِ یَنظُرُونَ
﴿٢٣﴾
A kan karagu, suna ta kallo.(23)
Tafseer:
تَعۡرِفُ فِی وُجُوهِهِمۡ نَضۡرَةَ ٱلنَّعِیمِ
﴿٢٤﴾
Kana sani a cikin fuskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.(24)
Tafseer:
یُسۡقَوۡنَ مِن رَّحِیقࣲ مَّخۡتُومٍ
﴿٢٥﴾
Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.(25)
Tafseer:
خِتَـٰمُهُۥ مِسۡكࣱۚ وَفِی ذَ ٰلِكَ فَلۡیَتَنَافَسِ ٱلۡمُتَنَـٰفِسُونَ
﴿٢٦﴾
¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.(26)
Tafseer:
وَمِزَاجُهُۥ مِن تَسۡنِیمٍ
﴿٢٧﴾
Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.(27)
Tafseer:
عَیۡنࣰا یَشۡرَبُ بِهَا ٱلۡمُقَرَّبُونَ
﴿٢٨﴾
(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.(28)
Tafseer:
إِنَّ ٱلَّذِینَ أَجۡرَمُواْ كَانُواْ مِنَ ٱلَّذِینَ ءَامَنُواْ یَضۡحَكُونَ
﴿٢٩﴾
Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.(29)
Tafseer:
وَإِذَا مَرُّواْ بِهِمۡ یَتَغَامَزُونَ
﴿٣٠﴾
Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.(30)
Tafseer:
وَإِذَا ٱنقَلَبُوۤاْ إِلَىٰۤ أَهۡلِهِمُ ٱنقَلَبُواْ فَكِهِینَ
﴿٣١﴾
Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.(31)
Tafseer:
وَإِذَا رَأَوۡهُمۡ قَالُوۤاْ إِنَّ هَـٰۤؤُلَاۤءِ لَضَاۤلُّونَ
﴿٣٢﴾
Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."(32)
Tafseer:
وَمَاۤ أُرۡسِلُواْ عَلَیۡهِمۡ حَـٰفِظِینَ
﴿٣٣﴾
Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.(33)
Tafseer:
فَٱلۡیَوۡمَ ٱلَّذِینَ ءَامَنُواْ مِنَ ٱلۡكُفَّارِ یَضۡحَكُونَ
﴿٣٤﴾
To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.(34)
Tafseer:
عَلَى ٱلۡأَرَاۤىِٕكِ یَنظُرُونَ
﴿٣٥﴾
A kan karagu, suna ta kallo.(35)
Tafseer:
هَلۡ ثُوِّبَ ٱلۡكُفَّارُ مَا كَانُواْ یَفۡعَلُونَ
﴿٣٦﴾
Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?*
* Amsar tambaya "na'am.".
(36)Tafseer: