This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah Al-Ghashiya (The Overwhelming).
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِیثُ ٱلۡغَـٰشِیَةِ
﴿١﴾
Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?(1)
Tafseer:
وُجُوهࣱ یَوۡمَىِٕذٍ خَـٰشِعَةٌ
﴿٢﴾
Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.(2)
Tafseer:
عَامِلَةࣱ نَّاصِبَةࣱ
﴿٣﴾
Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.(3)
Tafseer:
تَصۡلَىٰ نَارًا حَامِیَةࣰ
﴿٤﴾
Zã su shiga wata wuta mai zãfi.(4)
Tafseer:
تُسۡقَىٰ مِنۡ عَیۡنٍ ءَانِیَةࣲ
﴿٥﴾
Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.(5)
Tafseer:
لَّیۡسَ لَهُمۡ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِیعࣲ
﴿٦﴾
Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.(6)
Tafseer:
لَّا یُسۡمِنُ وَلَا یُغۡنِی مِن جُوعࣲ
﴿٧﴾
Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.(7)
Tafseer:
وُجُوهࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ نَّاعِمَةࣱ
﴿٨﴾
Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.(8)
Tafseer:
لِّسَعۡیِهَا رَاضِیَةࣱ
﴿٩﴾
Game da aikinsu, masu yarda ne.(9)
Tafseer:
فِی جَنَّةٍ عَالِیَةࣲ
﴿١٠﴾
(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.(10)
Tafseer:
لَّا تَسۡمَعُ فِیهَا لَـٰغِیَةࣰ
﴿١١﴾
Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.(11)
Tafseer:
فِیهَا عَیۡنࣱ جَارِیَةࣱ
﴿١٢﴾
A cikinta akwai marmaro mai gudãna.(12)
Tafseer:
فِیهَا سُرُرࣱ مَّرۡفُوعَةࣱ
﴿١٣﴾
A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.(13)
Tafseer:
وَأَكۡوَابࣱ مَّوۡضُوعَةࣱ
﴿١٤﴾
Da kõfuna ar'aje.(14)
Tafseer:
وَنَمَارِقُ مَصۡفُوفَةࣱ
﴿١٥﴾
Da filõli* jẽre,
* Matãsan kai.
(15)Tafseer:
وَزَرَابِیُّ مَبۡثُوثَةٌ
﴿١٦﴾
Da katifu shimfiɗe.(16)
Tafseer:
أَفَلَا یَنظُرُونَ إِلَى ٱلۡإِبِلِ كَیۡفَ خُلِقَتۡ
﴿١٧﴾
Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?(17)
Tafseer:
وَإِلَى ٱلسَّمَاۤءِ كَیۡفَ رُفِعَتۡ
﴿١٨﴾
Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?(18)
Tafseer:
وَإِلَى ٱلۡجِبَالِ كَیۡفَ نُصِبَتۡ
﴿١٩﴾
Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?(19)
Tafseer:
وَإِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَیۡفَ سُطِحَتۡ
﴿٢٠﴾
Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?(20)
Tafseer:
فَذَكِّرۡ إِنَّمَاۤ أَنتَ مُذَكِّرࣱ
﴿٢١﴾
sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.(21)
Tafseer:
لَّسۡتَ عَلَیۡهِم بِمُصَیۡطِرٍ
﴿٢٢﴾
Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.(22)
Tafseer:
إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ
﴿٢٣﴾
Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.(23)
Tafseer:
فَیُعَذِّبُهُ ٱللَّهُ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَكۡبَرَ
﴿٢٤﴾
To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.(24)
Tafseer:
إِنَّ إِلَیۡنَاۤ إِیَابَهُمۡ
﴿٢٥﴾
Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.(25)
Tafseer:
ثُمَّ إِنَّ عَلَیۡنَا حِسَابَهُم
﴿٢٦﴾
Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.(26)
Tafseer: