Surah Ad-Dhuha (The Forenoon)

Surah Ad-Dhuha (The Forenoon)

Hausa Translation11 Aya count
This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah Ad-Dhuha (The Forenoon).
وَٱلضُّحَىٰ ﴿١﴾
Inã rantsuwa da hantsi.(1)
Tafseer:
وَٱلَّیۡلِ إِذَا سَجَىٰ ﴿٢﴾
Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).(2)
Tafseer:
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ ﴿٣﴾
Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.(3)
Tafseer:
وَلَلۡـَٔاخِرَةُ خَیۡرࣱ لَّكَ مِنَ ٱلۡأُولَىٰ ﴿٤﴾
Kuma lalle ta ƙarshe* ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
* Ta ƙarshe, wãto, Lãhira; kuma ta farko, wato, dũniya.
(4)
Tafseer:
وَلَسَوۡفَ یُعۡطِیكَ رَبُّكَ فَتَرۡضَىٰۤ ﴿٥﴾
Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.(5)
Tafseer:
أَلَمۡ یَجِدۡكَ یَتِیمࣰا فَـَٔاوَىٰ ﴿٦﴾
Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?(6)
Tafseer:
وَوَجَدَكَ ضَاۤلࣰّا فَهَدَىٰ ﴿٧﴾
Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?(7)
Tafseer:
وَوَجَدَكَ عَاۤىِٕلࣰا فَأَغۡنَىٰ ﴿٨﴾
Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?(8)
Tafseer:
فَأَمَّا ٱلۡیَتِیمَ فَلَا تَقۡهَرۡ ﴿٩﴾
Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.(9)
Tafseer:
وَأَمَّا ٱلسَّاۤىِٕلَ فَلَا تَنۡهَرۡ ﴿١٠﴾
Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.(10)
Tafseer:
وَأَمَّا بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثۡ ﴿١١﴾
Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).(11)
Tafseer:

تسجيل الدخول / إنشاء حساب

أدخل بريدك الإلكتروني ليصلك رمز الدخول السريع (بدون كلمة مرور)