This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah Al-'adiyat (Those That Run).
وَٱلۡعَـٰدِیَـٰتِ ضَبۡحࣰا
﴿١﴾
Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.(1)
Tafseer:
فَٱلۡمُورِیَـٰتِ قَدۡحࣰا
﴿٢﴾
Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.(2)
Tafseer:
فَٱلۡمُغِیرَ ٰتِ صُبۡحࣰا
﴿٣﴾
Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.(3)
Tafseer:
فَأَثَرۡنَ بِهِۦ نَقۡعࣰا
﴿٤﴾
Sai su motsar da ƙũra game da shi.(4)
Tafseer:
فَوَسَطۡنَ بِهِۦ جَمۡعًا
﴿٥﴾
Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.(5)
Tafseer:
إِنَّ ٱلۡإِنسَـٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودࣱ
﴿٦﴾
Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.(6)
Tafseer:
وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَ ٰلِكَ لَشَهِیدࣱ
﴿٧﴾
Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka.(7)
Tafseer:
وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلۡخَیۡرِ لَشَدِیدٌ
﴿٨﴾
Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.(8)
Tafseer:
۞ أَفَلَا یَعۡلَمُ إِذَا بُعۡثِرَ مَا فِی ٱلۡقُبُورِ
﴿٩﴾
Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.(9)
Tafseer:
وَحُصِّلَ مَا فِی ٱلصُّدُورِ
﴿١٠﴾
Aka bayyana abin da ke cikin zukata.(10)
Tafseer:
إِنَّ رَبَّهُم بِهِمۡ یَوۡمَىِٕذࣲ لَّخَبِیرُۢ
﴿١١﴾
Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?(11)
Tafseer: