This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah Az-Zalzalah (The Earthquake).
إِذَا زُلۡزِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ زِلۡزَالَهَا
﴿١﴾
Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.(1)
Tafseer:
وَأَخۡرَجَتِ ٱلۡأَرۡضُ أَثۡقَالَهَا
﴿٢﴾
Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.(2)
Tafseer:
وَقَالَ ٱلۡإِنسَـٰنُ مَا لَهَا
﴿٣﴾
Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?"(3)
Tafseer:
یَوۡمَىِٕذࣲ تُحَدِّثُ أَخۡبَارَهَا
﴿٤﴾
A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.(4)
Tafseer:
بِأَنَّ رَبَّكَ أَوۡحَىٰ لَهَا
﴿٥﴾
cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.(5)
Tafseer:
یَوۡمَىِٕذࣲ یَصۡدُرُ ٱلنَّاسُ أَشۡتَاتࣰا لِّیُرَوۡاْ أَعۡمَـٰلَهُمۡ
﴿٦﴾
A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu.(6)
Tafseer:
فَمَن یَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٍ خَیۡرࣰا یَرَهُۥ
﴿٧﴾
To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.(7)
Tafseer:
وَمَن یَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةࣲ شَرࣰّا یَرَهُۥ
﴿٨﴾
Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.(8)
Tafseer: