Surah Al-Mursalat (Those sent forth)

Surah Al-Mursalat (Those sent forth)

Hausa Translation50 Aya count
This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah Al-Mursalat (Those sent forth).
وَٱلۡمُرۡسَلَـٰتِ عُرۡفࣰا ﴿١﴾
Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.(1)
Tafseer:
فَٱلۡعَـٰصِفَـٰتِ عَصۡفࣰا ﴿٢﴾
Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.(2)
Tafseer:
وَٱلنَّـٰشِرَ ٰ⁠تِ نَشۡرࣰا ﴿٣﴾
Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.(3)
Tafseer:
فَٱلۡفَـٰرِقَـٰتِ فَرۡقࣰا ﴿٤﴾
sa'an nan, da ãyõyi* mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
* Yã kamanta Manzanin Allah masu kãwo ayõyinsa da iskõki mãsu kãwo ruwa dõmin rahamar da ke cikin kowannensu.
(4)
Tafseer:
فَٱلۡمُلۡقِیَـٰتِ ذِكۡرًا ﴿٥﴾
Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.(5)
Tafseer:
عُذۡرًا أَوۡ نُذۡرًا ﴿٦﴾
Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.(6)
Tafseer:
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَ ٰ⁠قِعࣱ ﴿٧﴾
Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne(7)
Tafseer:
فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتۡ ﴿٨﴾
To, idan taurãri aka shãfe haskensu.(8)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلسَّمَاۤءُ فُرِجَتۡ ﴿٩﴾
Kuma, idan sama aka tsãge ta.(9)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ نُسِفَتۡ ﴿١٠﴾
Kuma, idan duwãtsu aka nike su.(10)
Tafseer:
وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتۡ ﴿١١﴾
Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.(11)
Tafseer:
لِأَیِّ یَوۡمٍ أُجِّلَتۡ ﴿١٢﴾
Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.(12)
Tafseer:
لِیَوۡمِ ٱلۡفَصۡلِ ﴿١٣﴾
Domin rãnar rarrabẽwa.*
* Yin hukunci a tsakanin tãlikai.
(13)
Tafseer:
وَمَاۤ أَدۡرَىٰكَ مَا یَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ ﴿١٤﴾
Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?(14)
Tafseer:
وَیۡلࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِینَ ﴿١٥﴾
Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!(15)
Tafseer:
أَلَمۡ نُهۡلِكِ ٱلۡأَوَّلِینَ ﴿١٦﴾
Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.(16)
Tafseer:
ثُمَّ نُتۡبِعُهُمُ ٱلۡـَٔاخِرِینَ ﴿١٧﴾
Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?(17)
Tafseer:
كَذَ ٰ⁠لِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِینَ ﴿١٨﴾
Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.(18)
Tafseer:
وَیۡلࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِینَ ﴿١٩﴾
Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!(19)
Tafseer:
أَلَمۡ نَخۡلُقكُّم مِّن مَّاۤءࣲ مَّهِینࣲ ﴿٢٠﴾
Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.(20)
Tafseer:
فَجَعَلۡنَـٰهُ فِی قَرَارࣲ مَّكِینٍ ﴿٢١﴾
Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.(21)
Tafseer:
إِلَىٰ قَدَرࣲ مَّعۡلُومࣲ ﴿٢٢﴾
Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.(22)
Tafseer:
فَقَدَرۡنَا فَنِعۡمَ ٱلۡقَـٰدِرُونَ ﴿٢٣﴾
Sa'an nan, Muka nũna iyãwar Mu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.(23)
Tafseer:
وَیۡلࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِینَ ﴿٢٤﴾
Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!(24)
Tafseer:
أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ كِفَاتًا ﴿٢٥﴾
Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.(25)
Tafseer:
أَحۡیَاۤءࣰ وَأَمۡوَ ٰ⁠تࣰا ﴿٢٦﴾
Ga rãyayyu da matattu,(26)
Tafseer:
وَجَعَلۡنَا فِیهَا رَوَ ٰ⁠سِیَ شَـٰمِخَـٰتࣲ وَأَسۡقَیۡنَـٰكُم مَّاۤءࣰ فُرَاتࣰا ﴿٢٧﴾
Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?(27)
Tafseer:
وَیۡلࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِینَ ﴿٢٨﴾
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!(28)
Tafseer:
ٱنطَلِقُوۤاْ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ ﴿٢٩﴾
Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!(29)
Tafseer:
ٱنطَلِقُوۤاْ إِلَىٰ ظِلࣲّ ذِی ثَلَـٰثِ شُعَبࣲ ﴿٣٠﴾
Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.(30)
Tafseer:
لَّا ظَلِیلࣲ وَلَا یُغۡنِی مِنَ ٱللَّهَبِ ﴿٣١﴾
Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.(31)
Tafseer:
إِنَّهَا تَرۡمِی بِشَرَرࣲ كَٱلۡقَصۡرِ ﴿٣٢﴾
Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.(32)
Tafseer:
كَأَنَّهُۥ جِمَـٰلَتࣱ صُفۡرࣱ ﴿٣٣﴾
Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.(33)
Tafseer:
وَیۡلࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِینَ ﴿٣٤﴾
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!(34)
Tafseer:
هَـٰذَا یَوۡمُ لَا یَنطِقُونَ ﴿٣٥﴾
Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.(35)
Tafseer:
وَلَا یُؤۡذَنُ لَهُمۡ فَیَعۡتَذِرُونَ ﴿٣٦﴾
Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.(36)
Tafseer:
وَیۡلࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِینَ ﴿٣٧﴾
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!(37)
Tafseer:
هَـٰذَا یَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِۖ جَمَعۡنَـٰكُمۡ وَٱلۡأَوَّلِینَ ﴿٣٨﴾
Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.(38)
Tafseer:
فَإِن كَانَ لَكُمۡ كَیۡدࣱ فَكِیدُونِ ﴿٣٩﴾
To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.(39)
Tafseer:
وَیۡلࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِینَ ﴿٤٠﴾
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!(40)
Tafseer:
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِینَ فِی ظِلَـٰلࣲ وَعُیُونࣲ ﴿٤١﴾
Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.(41)
Tafseer:
وَفَوَ ٰ⁠كِهَ مِمَّا یَشۡتَهُونَ ﴿٤٢﴾
Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.(42)
Tafseer:
كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِیۤـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ ﴿٤٣﴾
(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."(43)
Tafseer:
إِنَّا كَذَ ٰ⁠لِكَ نَجۡزِی ٱلۡمُحۡسِنِینَ ﴿٤٤﴾
Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.(44)
Tafseer:
وَیۡلࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِینَ ﴿٤٥﴾
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!(45)
Tafseer:
كُلُواْ وَتَمَتَّعُواْ قَلِیلًا إِنَّكُم مُّجۡرِمُونَ ﴿٤٦﴾
(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."(46)
Tafseer:
وَیۡلࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِینَ ﴿٤٧﴾
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!(47)
Tafseer:
وَإِذَا قِیلَ لَهُمُ ٱرۡكَعُواْ لَا یَرۡكَعُونَ ﴿٤٨﴾
Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."(48)
Tafseer:
وَیۡلࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِینَ ﴿٤٩﴾
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!(49)
Tafseer:
فَبِأَیِّ حَدِیثِۭ بَعۡدَهُۥ یُؤۡمِنُونَ ﴿٥٠﴾
To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni(50)
Tafseer:

تسجيل الدخول / إنشاء حساب

أدخل بريدك الإلكتروني ليصلك رمز الدخول السريع (بدون كلمة مرور)