Surah An-Naba' (The Great News)

Surah An-Naba' (The Great News)

Hausa Translation40 Aya count
This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah An-Naba' (The Great News).
عَمَّ یَتَسَاۤءَلُونَ ﴿١﴾
A kan mẽ suke tambayar jũna?(1)
Tafseer:
عَنِ ٱلنَّبَإِ ٱلۡعَظِیمِ ﴿٢﴾
A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?(2)
Tafseer:
ٱلَّذِی هُمۡ فِیهِ مُخۡتَلِفُونَ ﴿٣﴾
Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?(3)
Tafseer:
كَلَّا سَیَعۡلَمُونَ ﴿٤﴾
A'aha! Zã su sani.(4)
Tafseer:
ثُمَّ كَلَّا سَیَعۡلَمُونَ ﴿٥﴾
Kuma, a'aha! Zã su sani.(5)
Tafseer:
أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ مِهَـٰدࣰا ﴿٦﴾
Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?(6)
Tafseer:
وَٱلۡجِبَالَ أَوۡتَادࣰا ﴿٧﴾
Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?(7)
Tafseer:
وَخَلَقۡنَـٰكُمۡ أَزۡوَ ٰ⁠جࣰا ﴿٨﴾
Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?(8)
Tafseer:
وَجَعَلۡنَا نَوۡمَكُمۡ سُبَاتࣰا ﴿٩﴾
Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?(9)
Tafseer:
وَجَعَلۡنَا ٱلَّیۡلَ لِبَاسࣰا ﴿١٠﴾
Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?(10)
Tafseer:
وَجَعَلۡنَا ٱلنَّهَارَ مَعَاشࣰا ﴿١١﴾
Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?(11)
Tafseer:
وَبَنَیۡنَا فَوۡقَكُمۡ سَبۡعࣰا شِدَادࣰا ﴿١٢﴾
Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?(12)
Tafseer:
وَجَعَلۡنَا سِرَاجࣰا وَهَّاجࣰا ﴿١٣﴾
Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?(13)
Tafseer:
وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡمُعۡصِرَ ٰ⁠تِ مَاۤءࣰ ثَجَّاجࣰا ﴿١٤﴾
Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?(14)
Tafseer:
لِّنُخۡرِجَ بِهِۦ حَبࣰّا وَنَبَاتࣰا ﴿١٥﴾
Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?(15)
Tafseer:
وَجَنَّـٰتٍ أَلۡفَافًا ﴿١٦﴾
Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?(16)
Tafseer:
إِنَّ یَوۡمَ ٱلۡفَصۡلِ كَانَ مِیقَـٰتࣰا ﴿١٧﴾
Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.(17)
Tafseer:
یَوۡمَ یُنفَخُ فِی ٱلصُّورِ فَتَأۡتُونَ أَفۡوَاجࣰا ﴿١٨﴾
Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.(18)
Tafseer:
وَفُتِحَتِ ٱلسَّمَاۤءُ فَكَانَتۡ أَبۡوَ ٰ⁠بࣰا ﴿١٩﴾
Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.(19)
Tafseer:
وَسُیِّرَتِ ٱلۡجِبَالُ فَكَانَتۡ سَرَابًا ﴿٢٠﴾
Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.(20)
Tafseer:
إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتۡ مِرۡصَادࣰا ﴿٢١﴾
Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.(21)
Tafseer:
لِّلطَّـٰغِینَ مَـَٔابࣰا ﴿٢٢﴾
Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.(22)
Tafseer:
لَّـٰبِثِینَ فِیهَاۤ أَحۡقَابࣰا ﴿٢٣﴾
Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.(23)
Tafseer:
لَّا یَذُوقُونَ فِیهَا بَرۡدࣰا وَلَا شَرَابًا ﴿٢٤﴾
Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.(24)
Tafseer:
إِلَّا حَمِیمࣰا وَغَسَّاقࣰا ﴿٢٥﴾
Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.(25)
Tafseer:
جَزَاۤءࣰ وِفَاقًا ﴿٢٦﴾
Sakamako mai dãcẽwa.(26)
Tafseer:
إِنَّهُمۡ كَانُواْ لَا یَرۡجُونَ حِسَابࣰا ﴿٢٧﴾
Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.(27)
Tafseer:
وَكَذَّبُواْ بِـَٔایَـٰتِنَا كِذَّابࣰا ﴿٢٨﴾
Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, ƙaryatãwa!(28)
Tafseer:
وَكُلَّ شَیۡءٍ أَحۡصَیۡنَـٰهُ كِتَـٰبࣰا ﴿٢٩﴾
Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.(29)
Tafseer:
فَذُوقُواْ فَلَن نَّزِیدَكُمۡ إِلَّا عَذَابًا ﴿٣٠﴾
Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.(30)
Tafseer:
إِنَّ لِلۡمُتَّقِینَ مَفَازًا ﴿٣١﴾
Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.(31)
Tafseer:
حَدَاۤىِٕقَ وَأَعۡنَـٰبࣰا ﴿٣٢﴾
Lambuna da inabõbi.(32)
Tafseer:
وَكَوَاعِبَ أَتۡرَابࣰا ﴿٣٣﴾
Da yan Mata tsaraikun Juna(33)
Tafseer:
وَكَأۡسࣰا دِهَاقࣰا ﴿٣٤﴾
Da hinjãlan giya cikakku.(34)
Tafseer:
لَّا یَسۡمَعُونَ فِیهَا لَغۡوࣰا وَلَا كِذَّ ٰ⁠بࣰا ﴿٣٥﴾
Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.(35)
Tafseer:
جَزَاۤءࣰ مِّن رَّبِّكَ عَطَاۤءً حِسَابࣰا ﴿٣٦﴾
Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.(36)
Tafseer:
رَّبِّ ٱلسَّمَـٰوَ ٰ⁠تِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَیۡنَهُمَا ٱلرَّحۡمَـٰنِۖ لَا یَمۡلِكُونَ مِنۡهُ خِطَابࣰا ﴿٣٧﴾
Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.(37)
Tafseer:
یَوۡمَ یَقُومُ ٱلرُّوحُ وَٱلۡمَلَـٰۤىِٕكَةُ صَفࣰّاۖ لَّا یَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَـٰنُ وَقَالَ صَوَابࣰا ﴿٣٨﴾
Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.(38)
Tafseer:
ذَ ٰ⁠لِكَ ٱلۡیَوۡمُ ٱلۡحَقُّۖ فَمَن شَاۤءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا ﴿٣٩﴾
Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.(39)
Tafseer:
إِنَّاۤ أَنذَرۡنَـٰكُمۡ عَذَابࣰا قَرِیبࣰا یَوۡمَ یَنظُرُ ٱلۡمَرۡءُ مَا قَدَّمَتۡ یَدَاهُ وَیَقُولُ ٱلۡكَافِرُ یَـٰلَیۡتَنِی كُنتُ تُرَ ٰ⁠بَۢا ﴿٤٠﴾
Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"(40)
Tafseer:

تسجيل الدخول / إنشاء حساب

أدخل بريدك الإلكتروني ليصلك رمز الدخول السريع (بدون كلمة مرور)