Surah An-Nazi'at (Those who Pull Out)

Surah An-Nazi'at (Those who Pull Out)

Hausa Translation46 Aya count
This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah An-Nazi'at (Those who Pull Out).
وَٱلنَّـٰزِعَـٰتِ غَرۡقࣰا ﴿١﴾
Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.(1)
Tafseer:
وَٱلنَّـٰشِطَـٰتِ نَشۡطࣰا ﴿٢﴾
Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.(2)
Tafseer:
وَٱلسَّـٰبِحَـٰتِ سَبۡحࣰا ﴿٣﴾
Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.(3)
Tafseer:
فَٱلسَّـٰبِقَـٰتِ سَبۡقࣰا ﴿٤﴾
Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre.(4)
Tafseer:
فَٱلۡمُدَبِّرَ ٰ⁠تِ أَمۡرࣰا ﴿٥﴾
Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni.(5)
Tafseer:
یَوۡمَ تَرۡجُفُ ٱلرَّاجِفَةُ ﴿٦﴾
Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.(6)
Tafseer:
تَتۡبَعُهَا ٱلرَّادِفَةُ ﴿٧﴾
Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.(7)
Tafseer:
قُلُوبࣱ یَوۡمَىِٕذࣲ وَاجِفَةٌ ﴿٨﴾
Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.(8)
Tafseer:
أَبۡصَـٰرُهَا خَـٰشِعَةࣱ ﴿٩﴾
Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.(9)
Tafseer:
یَقُولُونَ أَءِنَّا لَمَرۡدُودُونَ فِی ٱلۡحَافِرَةِ ﴿١٠﴾
Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?(10)
Tafseer:
أَءِذَا كُنَّا عِظَـٰمࣰا نَّخِرَةࣰ ﴿١١﴾
"Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"(11)
Tafseer:
قَالُواْ تِلۡكَ إِذࣰا كَرَّةٌ خَاسِرَةࣱ ﴿١٢﴾
Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"(12)
Tafseer:
فَإِنَّمَا هِیَ زَجۡرَةࣱ وَ ٰ⁠حِدَةࣱ ﴿١٣﴾
To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.(13)
Tafseer:
فَإِذَا هُم بِٱلسَّاهِرَةِ ﴿١٤﴾
Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.(14)
Tafseer:
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِیثُ مُوسَىٰۤ ﴿١٥﴾
Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?(15)
Tafseer:
إِذۡ نَادَىٰهُ رَبُّهُۥ بِٱلۡوَادِ ٱلۡمُقَدَّسِ طُوًى ﴿١٦﴾
A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?(16)
Tafseer:
ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ ﴿١٧﴾
Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.(17)
Tafseer:
فَقُلۡ هَل لَّكَ إِلَىٰۤ أَن تَزَكَّىٰ ﴿١٨﴾
"Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.(18)
Tafseer:
وَأَهۡدِیَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخۡشَىٰ ﴿١٩﴾
"Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa?"(19)
Tafseer:
فَأَرَىٰهُ ٱلۡـَٔایَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰ ﴿٢٠﴾
Sai ya nũna masa ãyar* nan mafi girma.
* Ãyar Mũsã da ta fi girma ita ce sandarsa mai zama maciji ko hannunsa mai haske kamar tõcila idan yã sanya cikin hammata yã fitar.
(20)
Tafseer:
فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ ﴿٢١﴾
Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),(21)
Tafseer:
ثُمَّ أَدۡبَرَ یَسۡعَىٰ ﴿٢٢﴾
Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.(22)
Tafseer:
فَحَشَرَ فَنَادَىٰ ﴿٢٣﴾
Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.(23)
Tafseer:
فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلۡأَعۡلَىٰ ﴿٢٤﴾
Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."(24)
Tafseer:
فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلۡـَٔاخِرَةِ وَٱلۡأُولَىٰۤ ﴿٢٥﴾
Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.(25)
Tafseer:
إِنَّ فِی ذَ ٰ⁠لِكَ لَعِبۡرَةࣰ لِّمَن یَخۡشَىٰۤ ﴿٢٦﴾
Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.(26)
Tafseer:
ءَأَنتُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَمِ ٱلسَّمَاۤءُۚ بَنَىٰهَا ﴿٢٧﴾
Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.(27)
Tafseer:
رَفَعَ سَمۡكَهَا فَسَوَّىٰهَا ﴿٢٨﴾
Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.(28)
Tafseer:
وَأَغۡطَشَ لَیۡلَهَا وَأَخۡرَجَ ضُحَىٰهَا ﴿٢٩﴾
Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.(29)
Tafseer:
وَٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ ذَ ٰ⁠لِكَ دَحَىٰهَاۤ ﴿٣٠﴾
Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.(30)
Tafseer:
أَخۡرَجَ مِنۡهَا مَاۤءَهَا وَمَرۡعَىٰهَا ﴿٣١﴾
Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.(31)
Tafseer:
وَٱلۡجِبَالَ أَرۡسَىٰهَا ﴿٣٢﴾
Da duwatsu, Yã kafe ta.(32)
Tafseer:
مَتَـٰعࣰا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَـٰمِكُمۡ ﴿٣٣﴾
Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.(33)
Tafseer:
فَإِذَا جَاۤءَتِ ٱلطَّاۤمَّةُ ٱلۡكُبۡرَىٰ ﴿٣٤﴾
To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.(34)
Tafseer:
یَوۡمَ یَتَذَكَّرُ ٱلۡإِنسَـٰنُ مَا سَعَىٰ ﴿٣٥﴾
Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.(35)
Tafseer:
وَبُرِّزَتِ ٱلۡجَحِیمُ لِمَن یَرَىٰ ﴿٣٦﴾
Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.(36)
Tafseer:
فَأَمَّا مَن طَغَىٰ ﴿٣٧﴾
To, amma wanda ya yi girman kai.(37)
Tafseer:
وَءَاثَرَ ٱلۡحَیَوٰةَ ٱلدُّنۡیَا ﴿٣٨﴾
Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).(38)
Tafseer:
فَإِنَّ ٱلۡجَحِیمَ هِیَ ٱلۡمَأۡوَىٰ ﴿٣٩﴾
To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.(39)
Tafseer:
وَأَمَّا مَنۡ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ وَنَهَى ٱلنَّفۡسَ عَنِ ٱلۡهَوَىٰ ﴿٤٠﴾
Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.(40)
Tafseer:
فَإِنَّ ٱلۡجَنَّةَ هِیَ ٱلۡمَأۡوَىٰ ﴿٤١﴾
To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.(41)
Tafseer:
یَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَیَّانَ مُرۡسَىٰهَا ﴿٤٢﴾
Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?(42)
Tafseer:
فِیمَ أَنتَ مِن ذِكۡرَىٰهَاۤ ﴿٤٣﴾
Me ya haɗã ka da ambatonta?(43)
Tafseer:
إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَىٰهَاۤ ﴿٤٤﴾
Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.(44)
Tafseer:
إِنَّمَاۤ أَنتَ مُنذِرُ مَن یَخۡشَىٰهَا ﴿٤٥﴾
Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.(45)
Tafseer:
كَأَنَّهُمۡ یَوۡمَ یَرَوۡنَهَا لَمۡ یَلۡبَثُوۤاْ إِلَّا عَشِیَّةً أَوۡ ضُحَىٰهَا ﴿٤٦﴾
Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.(46)
Tafseer:

تسجيل الدخول / إنشاء حساب

أدخل بريدك الإلكتروني ليصلك رمز الدخول السريع (بدون كلمة مرور)