This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah At-Tin (The Fig).
وَٱلتِّینِ وَٱلزَّیۡتُونِ
﴿١﴾
Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.*
* Ibn Abbas ya ce: 'Attinu shi ne masallacin Nuhu a kan Judiyyi, Azzaitun Masallacin Baitil Muƙaddas.'.
(1)Tafseer:
وَطُورِ سِینِینَ
﴿٢﴾
Da Dũr Sĩnĩna.*
* Dutsen da Allah Ya yi magana da Musa a kansa. Ma'anarsa dutse mai albarka sabõda itacen da ke kansa.
(2)Tafseer:
وَهَـٰذَا ٱلۡبَلَدِ ٱلۡأَمِینِ
﴿٣﴾
Da wannan gari* amintacce.
* Gari amintacce shi ne Makkah.
(3)Tafseer:
لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَـٰنَ فِیۤ أَحۡسَنِ تَقۡوِیمࣲ
﴿٤﴾
Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.(4)
Tafseer:
ثُمَّ رَدَدۡنَـٰهُ أَسۡفَلَ سَـٰفِلِینَ
﴿٥﴾
Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni(5)
Tafseer:
إِلَّا ٱلَّذِینَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ فَلَهُمۡ أَجۡرٌ غَیۡرُ مَمۡنُونࣲ
﴿٦﴾
Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.(6)
Tafseer:
فَمَا یُكَذِّبُكَ بَعۡدُ بِٱلدِّینِ
﴿٧﴾
To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?(7)
Tafseer:
أَلَیۡسَ ٱللَّهُ بِأَحۡكَمِ ٱلۡحَـٰكِمِینَ
﴿٨﴾
Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?*
* Ana son wanda ya karanta sũrar har ƙarshe ya ce بلى ,wato na'am, Allah Ya fi kowa kyãwon hukunci.
(8)Tafseer: