Surah Al-'alaq (The Clot)

Surah Al-'alaq (The Clot)

Hausa Translation19 Aya count
This page contains the Arabic text, audio recitation, and Hausa translation of Surah Al-'alaq (The Clot).
ٱقۡرَأۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلَّذِی خَلَقَ ﴿١﴾
Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.(1)
Tafseer:
خَلَقَ ٱلۡإِنسَـٰنَ مِنۡ عَلَقٍ ﴿٢﴾
Ya hahitta mutum daga gudan jini.(2)
Tafseer:
ٱقۡرَأۡ وَرَبُّكَ ٱلۡأَكۡرَمُ ﴿٣﴾
Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci.(3)
Tafseer:
ٱلَّذِی عَلَّمَ بِٱلۡقَلَمِ ﴿٤﴾
Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.(4)
Tafseer:
عَلَّمَ ٱلۡإِنسَـٰنَ مَا لَمۡ یَعۡلَمۡ ﴿٥﴾
Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.(5)
Tafseer:
كَلَّاۤ إِنَّ ٱلۡإِنسَـٰنَ لَیَطۡغَىٰۤ ﴿٦﴾
A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).(6)
Tafseer:
أَن رَّءَاهُ ٱسۡتَغۡنَىٰۤ ﴿٧﴾
Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.(7)
Tafseer:
إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجۡعَىٰۤ ﴿٨﴾
Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.(8)
Tafseer:
أَرَءَیۡتَ ٱلَّذِی یَنۡهَىٰ ﴿٩﴾
Shin, kã ga wanda ke hana.(9)
Tafseer:
عَبۡدًا إِذَا صَلَّىٰۤ ﴿١٠﴾
Bãwã idan yã yi salla?(10)
Tafseer:
أَرَءَیۡتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلۡهُدَىٰۤ ﴿١١﴾
Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?(11)
Tafseer:
أَوۡ أَمَرَ بِٱلتَّقۡوَىٰۤ ﴿١٢﴾
Ko ya yi umurni da taƙawa?(12)
Tafseer:
أَرَءَیۡتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰۤ ﴿١٣﴾
Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?(13)
Tafseer:
أَلَمۡ یَعۡلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ یَرَىٰ ﴿١٤﴾
Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?(14)
Tafseer:
كَلَّا لَىِٕن لَّمۡ یَنتَهِ لَنَسۡفَعَۢا بِٱلنَّاصِیَةِ ﴿١٥﴾
A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.(15)
Tafseer:
نَاصِیَةࣲ كَـٰذِبَةٍ خَاطِئَةࣲ ﴿١٦﴾
Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.(16)
Tafseer:
فَلۡیَدۡعُ نَادِیَهُۥ ﴿١٧﴾
Sai ya kirayi ƙungiyarsa.(17)
Tafseer:
سَنَدۡعُ ٱلزَّبَانِیَةَ ﴿١٨﴾
Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).(18)
Tafseer:
كَلَّا لَا تُطِعۡهُ وَٱسۡجُدۡ وَٱقۡتَرِب ۩ ﴿١٩﴾
A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,* kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).
* Wato salla da sauran ibãdu.
(19)
Tafseer:

تسجيل الدخول / إنشاء حساب

أدخل بريدك الإلكتروني ليصلك رمز الدخول السريع (بدون كلمة مرور)